Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Mu’ujizozin Annabi (SAW) Da Suka Dara Na Annabi Harun, Yusuf, Dawud Da Sulaiman (Alaihimus Salam)

Published

on

Yana daga abin da Allah ya ba Annabi Harunu (AS), Allah ya ba shi fasahar magana. Shi kuwa Annabinmu (SAW) ya kasance mafi fasahar balaga ta inda duk mai duba Hadisansa (SAW) ba zai jahilci wannan ba. Kuma an ba Manzon Allah (SAW) kalma daya da take tattare abubuwa da yawa ta yadda mutane mabanbanta da sun ji, kowa zai ce da shi ake yi, don haka kake gani a karatuttuka ana fassara kalmarsa daya (SAW) da abubuwa da yawa, wasu su fassara da fahimta iri kaza, wasu kuma da wata fahimtar daban. Misali, Kibiya tana daga irin wadannan kalmomi. Mace mai kitso za ta ce tana amfani da Kibiya wurin kitso. Maharbi zai ce da Kibiya yake farauta. Idan mutum yana neman wani wuri za a yi masa kwatance da Kibiya, a ce ya duba zai ga wurin da Kibiya ta nuna; to nan ne wurin da yake nema. Wani zai iya cewa, ma’anar Kibiya sunan wani Gari ne a Kano. Wata kuma ta ce duk zance wadannan suke yi, abin da ake nufi da Kibiya zance ce, kamar wata ta ce wa kawarta idan kin taso daga wuri kaza “ki biya” mun sai mu wuce. Ka ga an yi ta shigar da ma’anonin Kibiya daban-daban a cikin zance. To haka, Manzon Allah (SAW) zai fadi kalma daya, sai Malamai su yi ta jujjuya ta a ma’anoni daban-daban, kuma kowacce ka dauka sai ka ga gaskiyarsu ce. Duba dai hatta masu fasahar technology na wannan zamanin, duk kwakwarsu suna dawowa su ce abin da Manzon Allah (SAW) ya fadi a wuri kaza; da su yake. Ka ga wannan yana daga Hikimar Manzon Allah (SAW).

Annabi Yusufa (AS) Allah ya ba shi kyau. Babu wani Annabi da Allah ya yi masa kyau irin Annabi Yusuf (AS). Amma duk da haka, Manzon Allah ya ce rabin kyauna aka ba shi. To me ya sa mata ba su yi wa Annabi (SAW) irin yadda suka yi wa Annabi Yusuf (AS) ba? Kyawon Annabi (AS) an cakuda shi ne da kwarjini. Ga kyan kana gani amma idan kana tare da shi har makyarkyata za ka iya yi saboda kwarjininsa (SAW). Da yawa mace za ta gan shi sai ta kama makyarkyata har sai Manzon Allah ya fada mata magana mai dadi sai ta natsu. Manzon Allah an ba shi kyau dukkansa. Duk wanda ya lura da irin siffofin Manzon Allah (SAW) da aka ciro (aka ruwaito) zai bayyana gare shi irin fifikon kyawon Manzon Allah (SAW) wanda ya hau dukkan kyau a cikin dukkan zamani.

Amma game da abin da Allah ya bai wa Annabi Yusufa (AS) na daga fassarar mafarkai, shi Annabi Yusufa (daga abin da aka ciato gare shi) ya fassara mafarkai guda uku. Ya fassara mafarkin sarki, shi ma an fassara masa mafarkin da ya ga taurari da rana da wata suna masa sujada, sannan ya fassara mafarkin abokan zamansa na kurkuku, mai dafa abinci da mai tatse wa sarki giya. Fassarar mafarki uku kenan da aka cirato. Amma shi kuwa Annabi (SAW) an ba shi fassarar mafarkin da ba za su kidayu ba. Duk wanda yake duba littafan Hadisai da na Tarihi zai samu a cikin fassarar mafarkin Manzon Allah (SAW) abubuwa na mamaki.

Amma game da abin da aka ba Annabi Dawudu (AS) na game da sarrafa karfe, yadda yake juya ta kamar gumba ko kamar tuwo saboda taushi ba tare da ya sa a wuta ba, shi ma an ba Annabinmu (SAW), Allah ya saukake masa zuciyoyin halitta masu tsauri, komai taurin zuciya idan ta zo gaban Annabi (SAW) sai ta yi taushi. Sarrafa karfe ya fi sauki a kan sarrafa zuciya, saboda zuciyoyin wasu mutanen sun fi dutse kekashewa (kamar yadda ya zo a cikin Suratul Bakara). Amma duk da haka idan suka zo gaban Annabi (SAW) sai su yi taushi. Kuma yana daga Mu’ujizar Manzon Allah (SAW) idan ya kama busasshen icce sai ya yi taushi ya koma danye har ya yi ganye. Kuma idan ya taka dutse komai kurmansa (karfinsa) sai kafarsa ta loba a ciki (SAW). Haka in ya jingina da dutse sai bayansa ya loba a ciki. Akwai inda ya yi sallah a kan dutse, alamar kafafuwansa da kwaurinsa da goshinsa da tafukan hannunsa duk suka fito. A da ana kiran wurin (da alamomin suka loba) da ‘Yan Akusa, yana bayan Baki’a (Makabartar Sahabbai), to amma shugabannin yanzu na Makka da suka zo an ce nakiya aka sa aka fasa dutsen ma gabakidaya. Kuma akwai inda Manzon Allah ya jingina a jikin dutsen Ukhudu sai da bayansa ya loba a ciki, Alhazai duk suna zuwa ziyara a wurin har zuwa kamar shekaru 50 baya, amma aka zo aka waragaza wai kar a ce an yi shirka, shafa wurin kawai fa, wai shi ne shirka (a wurinsu), Allah ya sauwaka.

Yana daga Mu’ujizar Annabi (SAW), ya shafi akuyar Ummu Ma’abadin wanda bunsuru bai taba bin ta ba (balle ta yi ciki) sai ga hantsarta ta sauka cike da nono, aka tatsa da yawa, Manzon Allah ya fara bai wa Ummu Ma’abadin ta sha sannan ya sha, daga nan ya ba Sayyidina Abubakar, sai Urai’ika (mai nuna musu hanya).

Amma game da abin da Allah ya ba Annabi Sulaiman (AS) na daga jin maganar tsuntsaye da horewar shaidanun aljannu (suna yi masa hidima kamar gine-gine da shiga rafi su debo masa lu’ulu’u), da horewar iska da ke daukarsa da tawagarsa (a kan wata shimfida da aljannu suka yi masa da ke iya daukarsa da duk mutanensa da abubuwan amfaninsu irin su tukwane da sauransu), kuma Allah ya ba shi mulkin da ba zai bai wa wani da ba bayansa har duniya ta nade. To, shi ma Annabi (SAW) an ba shi irin wannan har da kari. Game da jin maganar tsuntsaye da namun daji da na gida ma da aka bai wa Annabi Sulaimanu (AS), shi Manzon Allah (SAW) dutse ne ya yi masa magana, wannan ya fi ban mamaki; domin tsuntsu dai yana da rai yana motsawa, yana ma kuka da bakinsa (duk da maganarsa mu’ujiza ce) amma maganar dutse ta fi ban mamaki. Manzon Allah (SAW) ya ce “na san wani dutse a Makka), duk idan na zo shigewa sai ya yi mun sallama (wasu malamai sun ce dutsen Hajrul As’wadu ne, wasu kuma suka ce dutsen Aba Kubaisi ne). Haka nan Manzon Allah ya debi tsakwankwani sai suka kama Tasbihi a hannunsa. Ka ga wannan sandararren abu ne amma sai ga shi ya yi magana, wannan ya fi ban mamaki. Sannan karfatar akuya wadda aka sa wa guba aka dafa ta, ita ma ta yi wa Manzon Allah (SAW) magana. Ko danya ce karfatar, aka yanka akuya aka cire sannan aka dafa kuma ta yi magana, ai wannan ya isa abin mamaki. Haka nan barewa ta yi magana da Annabi (SAW). Rakumi ma ya yi magana da Annabi (SAW). Sannan damo da aka yanka, shi ma ya yi magana da Annabi (SAW). A kan batun damon nan, wani mafarauci ne ya ce wa Manzon Allah ba zai yi imani da shi ba har sai damon da ya farauto ya yanka (har ma ya cire lakarsa) ya yi magana, shikenan Manzon Allah ya sa damon ya yi magana.

Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a makon gobe, in sha Allahu. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: