Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Mu’ujizozin Annabi (SAW) Da Suka Dara Na Annabi Sulaiman (AS)

Published

on

Masu karatu assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata a karshen darasinmu muna bayani ne a kan mu’ujizar jin maganar tsuntsaye da aka bai wa Annabi Sulaimanu (AS), wanda shi ma Manzon Allah (SAW) an ba shi ita har da kari, inda muka kawo maganar da ya yi da rakumi da damo har ma da yadda sandararrun abubuwa da babu jini a jikinsu irin tsakuwa da dutse da suke wa Manzon Allah (SAW) magana. Za mu dora daga nan, in sha Allah.
An ruwaito cewa wani tsuntsu an yi masa bara’uwa da dansa, yara suka hau shekarsa suka dauke masa da, tsuntsun nan ya zo ya rika buga kansa a jikin Annabi (SAW) yana yi masa magana. Sai Manzon Allah (SAW) ya tambaya; waye ya dau wa wannan tsuntsu dansa, sai wani mutum ya ce “ni ne, ya Rasulullah (SAW)”, sai Annabi ya ce ya mayar masa da dansa. Bukhari da Abu Dawuda duk sun fitar da wannan Hadisin. Jin maganar tsuntsaye ba ma Annabi (SAW) ba da kansa, akwai wani Sahabi da ya ce bayan Annabi (SAW) ya ta fi ya bar mu, ba wani tsuntsu da zai buga fukafukinsa (a wurinsu) face sun san me yake cewa. Kura ta yi wa mutane magana da yawa, akwai wani makiyayi da yake kiwo kura ta yi ta kawo wa tumakinsa bara (kai-kamu) yana korar ta, har dai ya gaji ya ce “kai wannan kura kin cika naci”, sai kurar nan ta amsa da cewa, “ai kai ne ka cika naci, ga Annabin karshen zamani can ya bayyana amma ka ki zuwa ka yi imani da shi wai kai kana kiwo”, makiyayin ya ce “to, wa zai rike mun dabbobina in tafi wurinsa?”, kura ta ce “ga ni zan rike maka kuma ba zan taba ba”. Makiyayin nan ya ce tun da dai har kurar nan ta yi magana ya san wani abu ne daga Allah. Shikenan ya tafi ya ba da gaskiya da Annabi (SAW) kuma ya fada masa zancen kurar. Manzon Allah (SAW) ya ce masa, “ko ma ka gani, ba ta taba komai ba, amma idan ka je ka yanka mata daya mana”. Makiyayi ya koma ya ga kura ba taba masa ko dabba daya ba. Kura ta ce za ta tafi, ya ce mata a’a, Manzon Allah ya ce ya yanka mata daya. Ya yanka mata, kura ta dauka ta yi daji. Haka nan akwai wani malami bawan Allah wanda ya ji kerkeci ya yi kuka sau biyu, sai (Malamin) ya ce “Allahu Akbar”, aka tambaye shi mene ne? Malamin ya ce “kerkecin ya fada mun cewa da ni; da wane da wane, shekarar ajalinmu ta kama”, kuma an tabbatar duk a wannan shekarar suka rasu. Ka ga hatta a cikin malaman al’ummar Annabi (SAW) ma an samu masu jin maganar dabbobi.
Amma game da iska da Allah ya hore wa Annabi Sulaimanu (AS) wacce a tafiyar safiya kadai takan yi tafiyar tsawon wata guda, haka nan a tafiyar yamma ma tana yin tafiyar wata, ta dau Annabi Sulaiman da abincin rundunarsa da dawakinsu da sauran kayan amfaninsu zuwa duk inda yake so ya kewaya kasashe, shi ma Annabi (SAW) Allah ya ba shi Buraka wadda ta fi iska sauri, ba ma iska ba Buraka ta fi walkiya sauri. Shi ya sa aka sanya mata sunan Buraka, wanda ya samo asali daga “Barku” ma’ana “Walkiya” da ke walkatawa. Kuma Allah ya nuna al’ummar Manzon Allah (SAW) za ta rika hawa jirgi kuma ikon Allah su dai Bani Isra’ilan nan da iska ke daukar kakanninsu su ne suke kera jirgin. Bayan Buraka, har ila yau Mi’iraji ya dauki Manzon Allah (SAW) daga kan kasa zuwa Al’arshi, a kiftawa kawai an haye duka sama, wanda tafiyar shekara dubu bakwai ce. Wannan ma tafiyar sammai ce kawai, amma da aka bar sammai aka fara tafiyar Rafrafu wannan ba wanda ya san adadin nisan tafiyar sai Allah Tabaraka wa Ta’ala. Annabi Sulaiman (AS) an hore masa iska ce ta rika daukarsa zuwa sassan doron kasa. Amma shi kuwa Annabi (SAW) an cure masa duniya da lahira a gabansa yana kallonsu, yana zaune sai ka ji yana cewa ya ga kaza, ya sa hannunsa a kaza, ya ci kaza da dai sauransu, har Manzon Allah ya ga mahudar rana da mafadarta. Ka ga akwai bambanci a tsakanin wanda ya je sassan doron kasa, watau Annabi Sulaiman da kuma wanda yana zaune sassan duniya ta zo masa, watau Annabi (SAW). Ba tun yanzu ne aka fara batun dunkulewar duniya wuri guda ba (kamar yadda Turawa suka hade duniya bai-daya a shafin intanet a yau). Manzon Allah (SAW) shi ne farkon wanda ya tattara duniya bakidaya a dunkule wuri daya.
Amma game da abin da aka bai wa Annabi Sulaimanu (AS) na Allah ya hore masa shaidanu yana yin abin da ya so da su, shi ma Manzon Allah (SAW) an ruwaito ya tashi cikin dare zai yi sallah, sai wani shaidani ya zo da tartsatsin wuta zai kona fuskar Annabi (SAW), sai Allah ya ba shi dama ya kama shaidanin ya daure shi a jikin ginshikin masallaci. Manzon Allah ya ce ya yi niyya da safe ya nuna wa yaran Madina wannan shaidanin su yi wasa da shi, amma sai ya tuna wannan aikin Sulaimanu ne ba nashi ba. Annabi Sulaimanu ya roki Allah ya ba shi mulkin da bai dace ga wani bayansa ba. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce ya yi ladabi ga Sulaimanu a kan haka, domin abin da Allah ya ba shi ya ishe shi ba sai ya yi irin na wani ba. Shikenan Manzon Allah (SAW) ya kwance shaidanin. Annabi Sulaimanu (AS) Aljannu ne suka yi masa hidima, shi kuma Annabi (SAW) an hore masa Mala’iku ne suna masa hidima.
Allah ya ba Manzon Allah (SAW) abin da ya fi na Annabi Sulaiman (AS) na daga imanin Aljannu. Annabi Sulaimanu yana sarrafa Aljannunsa ne saboda tsoronsa da suke ji, yayin da suka gane (Annabi Sulaimanu) ya mutu, sai duk suka watse gabakidaya. Amma shi kuwa Manzon Allah (SAW) yana sallah a Wadin Nakalata, Aljannun Nasibina suka zo suka yi imani da shi, kuma ya tura su cikin jama’arsu su je su yi kira zuwa ga Allah. Tun daga rannan, an samu manyan sahabban Manzon Allah a cikin Aljannu, wasu sun rasu, wasu kuma har yau suna nan da ransu. Kuma yadda muke da rabe-rabe a cikin mu mutane, akwai musulmi da kafirai, da masu kudi da talakwa, da malamai da waliyyai da jahilai, a cikin Aljannu ma akwai haka.
Amma dangane da kididdige Aljannu cewa su ma rundunar Annabi Sulaimanu (AS) ne, Manzon Allah (SAW) ma an ba shi fiye da wannan, domin Allah ya kirga Mala’iku a matsayin suna cikin rundunar Manzon Allah. Mala’ika Jibrilu (AS) da wanda yake tare da shi suna daga cikin rundunarsa (SAW). idan aka lura da batun yaki kuma, don a kara yawan rundunar Manzon Allah, Allah ya ce (akwai) Mala’iku dubu biyar a cikin rundunar da Allah ya aike masa (SAW).
Amma game da batun tsuntsaye da aka hore wa Annabi Sulaimanu a cikin rundunarsa, Manzon Allah ma an hore masa, ya shiga kogo sai kurciya maza-maza ta zo ta shiga ta yi sheka, gizigizo ma ya zo ya yi saka a bakin kogon don su ba da kariya ga Manzon Allah daga makiyansa. Wani dan sarkin karya (a cikin wadanda suka bi sawu) ya zo ya ce wannan yanar gizogizon tun kafin a haifi mahaifiyar Manzon Allah yake a nan wurin. An ambaci yawan runduna ne domin nuna karfin ba da kariya ga Annabi Sulaimanu, amma shi kuwa Manzon Allah (SAW) Allah ya tsare shi da ‘yan kananan abubuwa, dubi dai yadda kurciya da gizogizo suka zo suka kare shi daga wadannan kafiran.
Amma game da abin da aka ba Annabi Sulaimanu (AS) na daga mulki, shi Manzon Allah (SAW) an ba shi zabi ne a kan ko ya zama Annabi Sarki ko Annabi Attijiri ko Annabi Bawa, Manzon Allah ya zabi ya zama Annabi Bawa (shi ba mai sarauta ba kuma ba hamshakin attijiri ba). Amma kuma Manzon Allah (SAW) Allah ya ba shi; shi ne Sarki a cikin sahabbansa da ma dukkan musulmi. Domin duk da sarakunan garuruwa da shugabannin dauloli suna nan, mu musulmi muna ji a ranmu cewa Manzon Allah (SAW) shi ne gaba da su. Irin wannan sarauta tasa (SAW) ta shafi hatta malaman da suka bi shi, shi ya sa duk wanda ya rataya da wani abu na Manzon Allah za ka ga ana bin sa duk da cewa shi ba sarki ne na gari ba. Mulkin Manzon Allah ba na tara sojoji da makamai da dukiyar kasa ba ce, amma kuma ko shi kadai aka ga yana tafiya, za a ga kwarjini na duk wadannan abubuwa a tare da shi (SAW).
Annabi Sulaimanu (AS) idan ya zauna tsuntsaye ne suke zuwa su yi masa rumfa, shi kuwa Annabi (SAW) girgije (Hadari) ne ke zuwa ya yi masa, duk inda yake girgije yana bin sa yana masa inuwa. Akwai Masjidul Gamami (Masallacin Girgije) a dan gaba da masallacinsa (na Madina) kadan. Manzon Allah ya yi sallar idi a nan wajen, yayin da rana ta daga kadan sai girgije ya zo ya yi masa rumfa, sai aka sa wa wajen sunan “Masallacin Girgije”.

Advertisement

labarai