Connect with us

RIGAR 'YANCI

N-Power: AYC Ta Yi Tir Da Yunkurin bata Wa Sanata Lawan Suna

Published

on

Gamayyar kungiyoyin Matsan Arewacin Nijeriya a karkashin inuwar kungiyar Matsa ta AYC, sun yi tir da masu yunkurin batawa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan suna.

Shugaban kungiyar AYC na kasa kuma mai magana da yawun sauran kungiyoyin na matasan Arewa Kwamarade Mukhtar Muhammad ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da suka fitar jin kadan bayan kungiyoyin sun kammala taron gaggawa a Kaduna.

Kwamarade Mukhtar Muhammad yana mayar da martani ne kan wani rahoto da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta wallafa, inda ta ce an bai wa Sanata Ahmad Lawan gurabe a aikin N-Power da ake shirin daukan matasa a yanzu.

A cewar shugaban Kwamarade Mukhtar Muhammad, wannan shaci fadi ne tsagwaronsa kuma anyi hakan ne da nufin batawa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan suna don cimma wata manufa ta siyasa.

Kwamred Mukhtar Muhammad ya kuma bukaci kafar data gaggauta neman afuwa daga Sanata Ahmad Lawan kan labaran nata na kanzon kurege da kuma janye labaran mars tushe balle makama.

Shugaban Kwamarade Mukhtar Muhammad ya yi nuni da cewa, Shugaban Majaliksar bawai yana wakiltar mazabarsa bane kawai idan akayi la’kari da kujerrar da ya ke akai.ta shugaban majalisa, yana shugabantar Nijeriya ce baki daya.

A cewar Kwamarade Mukhtar Muhammad, bai kamata ba a yayin da Sanata Ahmad Lawan ya ke gudanar da kyakyawan shugabanci a majalisa wasu kuma su fito.da wata sabuwar hanyar neman bata masa suna duk.da yunkurin hakan da suka yi a baya yaci tura.

Bugu fa kari, Muhammad, ya kuma yi kira ga al’umma da su yi watsi da wannan rahotanni masu yaduwa na cewa an ba Shugban Majalisar Sanata Ahmad Lawan gurabe a aikin shirin N-Power da za a dauki matasa.

A karshe, shugaban Kwamarade Mukhtar Muhammad ya yi kira ga kafofin yada labarai da ke a kasar nan, mysamman na shoshiyal mediya dasu dinga yada rahotanni na gaskiya bana kage ko son batawa manyan kasar nan suna kamar su Sanata Ahmad Lawan ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: