Dan kwallon Brazil, Neymar ya ce yanzu batun makomarsa a Paris St Germain kan tsawaita zamansa a Faransa ba wani babban lamari ba ne da ke jan hankali kuma tuni ya amince zai ci gaba da zaman kungiyar.
A shekarar 2017, Paris St Germain ta dauki Neymar daga Barcelona kan dalar Amurka miliyan 265.60 a matakin mafi tsada a fannin kwallon kafa a duniya kuma har yanzu ba’a sayi dan wasa mai tsadar sa ba.
Dan kwallon tawagar Brazil din ya ci Ligue 1 uku da French Cup biyu tun komawarsa Faransa da buga wasa, kuma ya taka rawar gani da PSG ta kai wasan karshe a Champions League a bara duk da cewa sunyi rashin nasara a hannun Bayern Munchen.
Neymar wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen Yunin badi, ya kira kungiyar ta Faransa da cewa gida ce a wurinsa kuma zaiyi iya yinsa wajen ganin ya taimakawa kungiyar wajen lashe kowanne irin kofi.
Tuni dan wasa Neymar ya ci wa PSG kwallo shida a gasar Zakarun Turai da ake buga wa, shi kuwa Kylian Mbappe ya zura takwas a raga a kuma a ranar Talata PSG ta kai wasan daf da karshe a Champions League na bana, duk da doke ta 1-0 da Bayern Munich ta yi a Faransa.
Ranar Laraba kungiyar ta Faransa ta je ta ci Bayern Munich 3-2 a wasan zagayen farko a kuarter final a Jamus wanda wannan sakamakon wasan shine ya basu damar doke masu kare kambun, wato Bayern Munchen.