Connect with us

NAZARI

Na Bar Aiki A Muryar Amurka Don In Kasance Kusa Da Mahaifiyata A Nijeriya —Umar Sa’idu Tudun Wada

Published

on

Gabatarwa

Masu karatunmu wannan ita ce tattaunawar da Editanmu Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki, ya yi da kwararre kuma fataccen Dan jaridar nan, shugaban Gidan rediyon jihar Kano (Bello Dandago), Alhaji Umar Sa’idu Tudun Wada, a ofishinsa da ke harabar Gidan  rediyon a Jalla Babbar Hausa. Kasancewar Alhaji Umar Sa’idu Tudun Wada ba ya bukatar gabatarwa, don haka sai mu ce wa masu karatunmu ga fili ga mai doki:

 

Tarihina

Suanana Umar Sa’idu Tudun Wada. Ahalin yanzu ni ne shugaban Gidan rediyon jihar Kano (Bello Dandago). An haife ni ranar 21, ga watan Oktoba shekara ta 1960, a garin Tudun Wadar Dankadai da ke jihar Kano. Na yi makarantar firamare a garin Tudun Wada, daga shekara ta 1967 zuwa 1973. Na yi sakandire a Gobernment College Kano, da ake cewa Rumfa College daga  sheka ta 1974 zuwa 1979, bayan na gama sakandire, sai na yi koyarwa na shekara daya a Wudil watau 1979 zuwa 1980.

Daga nan na dawo Kano na fara aiki a a ma’iakatar ayyuka da gidaje, daga nan sai na samu aiki a gidan Talabajin na NTA da ke Kano. Lokacin daman tun ina makaranta ina da sha’awar aiki  a kafar yada labarai, saboda haka, tun muna makaranta muka kai takardarmu ta neman aiki a NTA, muna jarrabawa. Da muka fita kuma bayan wannan shekara dayan, sakamakon jarrabawa ya fito aka dauke mu. Saboda haka ni daga lokacin da na fara aiki a dakin labarai na gidan talabijin na NTA, ilimin sakandire nake da shi, to amma kuma ina aikin aka bar ni na koma makaranta. Akwai makarantu da ke horas da kwarewa a kan aikin kawai, watau ba academic ba,irin su wata cibiyar horas da ‘yan jarida da ke Legas (Insititute Of Journalism Lagos)  bayan na kammala wannan kwas a wannan makaranta, sai kuma na tafi jami’ar Bayero inda na karanta Public Administration, sannan na je na yi wata Diploma a Kano kan al’amuran da suka shafi raya kasa watau Debelopment Studies.

Bayan wadannan na yi wasu kwasa-kwasai wasu a nan gida Nijeriya wasu kuma a kasashen waje, wannan su ne abin da na dan taba ta fuskar karatu.

Ta fuskar aiki kuma, bayan na yi shekara uku a NTA Kano. A shkara ta 1983 sai na dawo gidan Talabijin na CTB, a nan an dauke ni a matsayin mai dauko labarai. Na yi aiki a nan na tsawon shekara goma sha takwas.

Lokacin da na bar aiki a nan, na kai matsayin principal current affairs officer. Ina wannan aikin sai na ji na gaji da shi, saboda babu wani kalubale, kullum abin da ka saba abu dayan nan shi za ka yi, in ka zo da safe a tura masu dauko labarai, su je su dauko labarai ka gyara. Saboda da na ga na yi shekara goma sha takwas ina ta abu daya, sai na ji abin ya dame ni.

Saboda haka zsai na shirya barin aiki, domin in zauna zaman kaina. Na bar aiki bayan shekara daya, ina zaman kaina, kuma ina rahoto ga Muryar Jama’ar Jamus. Ina cikin wannan sai aka ba ni mataimakin daraktan yada labarai na gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Daga baya kuma aka mai da shi matimaki na musamman a kan harkar yada labarai.

Bayan na gama sai na ci gaba da aiki a Docebele. Daga baya a shekara ta 2003, sai aka bude Gidan rediyon Freedom. Sai aka neme ni da in zo domin kasancewa daya daga cikin jagorori na farko da za su bude wannan Gidan rediyo. Saboda haka muka zo muka fara aiki har zuwa shekara ta 2006. Na rike mataimakin babban manaja mai kula da ayyukan yau da kullum. Ni ne nakae kula da shirye-shirye da kuma sashin labarai da al’amuran yau da kullum.

Bayan na shekara uku ina wannan aiki, sai kuma na samu aiki a Muryar Amurka, sai na tafi Washinton, a matsayin jami’in yada labarai na kasa da kasa(International Broadcaster). Nan ma da na shekara uku, duk da cewa aiki ne na dindindin, shi ma sai na ji na fara gajiya da aikin, duk da cewa yanayin aikin na da kyau kuma akwai albashi mai tsoka.

Amma a lokacin ina da mahaifiyata, ta tsufa, kuma ina da iyali, sai cewa na kasa daure a ce sau daya zan zo in ga mahaifiyata a shekara in na zo hutu, ni kuma ban riga na zama dan kasar can ba, ballantana in tafi da ita tare da iyalina ba. Saboda haka da na kasa daure wannan shi ma sai na ajiye aikin. Sai na dawo gida Nijeriya.

Lokacin da na dawo, Babban manajan da muka fara aikin Gidan rediyon Freedom da shi, lokacin ya rasu, Allah ya jikansa. Su kuma gidan rediyon Freedom sun bi ni har Washinton, don Allah in daure mana in dawo, in ci gaba aiki a nan. Saboda haka sai na dawo a matsayin babban manaja. Ina nan har shekara ta 2016. Na rike babban manaja har shekara ta 2015, a wannan shekarar aka yi min karin girma na zama mataimakin manajan Darakata. A nan na shekara daya.

Daga sai na ji ina da sha’awar in gwada zaman kaina. Saboda haka sai na ajiye aiki. Na kafa wani karamin kamfani na sa masa suna Amara. Shi wannan kamfani yana samar da shirye-shirye irin na rediyo da talabijin ko kuma decumentry. Kuma mukan samar da shiri mu sayarwa da gidajen rediyo. Shi ma wannan kamfanin har yanzu yana nan.

Ina cikin haka sai wata hukumar raya kasashe ta kasar Birtaniya, sai suka ba ni aiki a matsayin jami’in tuntuba a fannin horas da ‘yan jarida. Ita wannan hukuma tana da yarjejeniya da wasu kafofin yada labarai, a Kaduna da Jigawa da Kano da Katsina, za mu je mu samu ma’aikatansu da ke gabatar da shirye-shirye, mu horas da su a kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen. Shi ma muka yi aikin duka cewa a tsari shekara uku ya kamata mu yi muna wannan aikin, amma sai aka samu matsala bayan shekara daya sai suka rufe wannan shirin.Da aka rufe sai na dawo na ci gaba da aiki a kamfanina na Amara.

Ana cikin haka sai gwamnatin jihar Kano ta nemi in zo in zama mai bai wa gwamna shawara na musamman a fannin yada labarai. Na zo kwana uku da fara aiki, sai aka ga cewar gidan rediyon Kano ya kamata in zo, domin akwai matsalolin da ake ganin in na je zan daidaita su. Lokacin da na zo redoyn FM na Tukuntawa bat a fitar da sauti sosai ta Jogana kuma ba ta  yi ma gaba daya.

Cikin ikon Allah da na dawo, ta Tukuntawar ta gyaru ita ma ta Joganar ta dawo ta ci gaba da aiki, kuma a halin yanzu, suna nan suna ci gaba da aiki kuma kullum muna kara lalubo hanyoyin da za a kara inaganta aikace-aikacen wannan Gidan rediyo. Mai karatu a tare mu a mako na gaba don jin kalubalen da bakon namu ya fuskanta a matakai daban-daban na rayuwarsa, da ma sauran wasu bayanai masu amfani.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: