Na Daina Siyasar Jam’iyya Har Abada – Obasanjo

Obasanjo

Daga Yusuf Shuaibu

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya daina siyasa har abada sannan bai da nufin kafa wata sabuwar jam’iyyar siyasa kar yadda wasu kafafan yada labarai suke ta yayatawa. Wannan yana cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin mai taken ‘Obasanjo ba zai kafa wata jam’iyya ba’. Sanarwar tana dauke ne da sahannun mai taimawa tsohon shugaban kasar ta fannin yada labarai, Kehinde Akinyemi.

Akinyemi ya bayyana cewa a yanzu haka maigidansa yana Kabul na kasar Afghanistan a matsayin babban makon shugaban kasa Ashraf Ghani, ya ce rahoton ba gaskiya ba ne tare da bayyana cewa babu shirin kafa wata sabuwar jam’iyya a yanzu ko kuma nan gaba.

Obasanjo ya bayyana cewa, “a nawa ra’ayi ba zan taba amai sannan in lashe ba. idan na ce na bar abu to ba zan sake dawo kan shi ba. Wadanda suka kitsa abun kila ma sun shude. Sannan wadanda suka yarda da wannan labari, to idan an ce iyayensu mata maza ne za su yarda.

“Na gama siyasa, amma matsayina a Nijeriya da kuma Afirka ba zai lissafu ba, sanna kofata a fude take ga kowani mutum ko kungiya wadanda suke neman taimakona ko shawarwari a kan duk wani abu, zan saurare su dai-dai bakin iko ba tare da nuna wani banbanci ba.

“Idan Cif Obasanjo na da wani jam’iyyar siyasa bai wuce jam’iyyar ‘yan Nijeriya da suke fuskanta na rashin tsaro da rashin aikin yi da yunwa da talauci da sauran matsaloli da dama. Wannan shi ne jam’iyyar da zai ceto Nijeriya da kara hadin kai da zama lafiya da samun tsaro da adalci da ci gaba mai dorewa.

“Wadanda suke kokarin bi ta baya domin dawowa da Cif Obasanjo cikin harkokin siyasa sun kasance makiyarsa. A wannan bangare, tsohon shugaban kasan zai ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyarsa na bayar da shawarwari da goyan baya ko kawo mafita ga Nijeriya da Afirka da ma duniya baki daya.”

Obasanjo shi ne shugaban kasan Nijeriya wanda aka zaba ta hanyar dimokaradiyya a tsakanin ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999 da ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ya lashe zabe ne a karkashin inuwar jam’iyyar PDP lokacin da Nijeriya ta sake dawowa mulkin farar hula bayan wasu shekarun da sojoji suka kwashe suna mulki. Kafin wannan lokaci, Obasanjo shi ne shugaban kasa na mulkin sojo a tsakanin ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976 zuwa ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 1979. Tun lokacin da ya bai karagar mulki, Obasanjo ya koma gidansa da ke Oke Mosan na Abeokuta cikin Jihar Ogun, yana yawan yin magana a kan manyan batutuwan da ya shafi kasa da na kasashen waje na ilmantarwa kan rashin tsaro da kuma na tattalin arziki.

Exit mobile version