Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Sakamakon wani rikici da ya taso tsakanin shugaban karamar hukumar Kontagora, Hon. Attahiru Ahmed (Baban Makaranta) da kansilolinsa wadanda suka zarge shi da boye musu gaskiyar yadda kudaden shigar karamar hukumar ke shiga ya zo karshe.
Tun farko dai kansilolin sun rubuta takardar dakatarwa ne da nufin sai gwamnatin jiha ta nada kwamiti don yin bincike korafe-korafensu, inda suka umurci mataimakinsa ya dare kan kujerar shugabancin karamar hukumar a matsayin mai rikon kwarya. Bayan kokarin shiga tsakani da masu ruwa da tsaki a matakin karamar hukuma abin ya citura, sai uwar jam’iyya ta karbi ragamar yin sulhu da samun dai-daito tsakanin bangarorin biyu.
Ranar Littinin din da ta gabata aka zauna tsakanin bangarorin biyu da shugabancin jam’iyyar APC ta jiha, inda shugaban jam’iyyar ta jiha Injiniya Muhammad Imam ya jagoranci zaman, bayan tsawon lokaci da aka dauka a kan teburin shawara, wanda ake tuhumar, wato shugaban karamar hukumar ya amshi laifinsa a wasu korafe-korafen da majalisar kansilolin ta gabatar tare da yin alkawarin zai dawo da wasu kudade da ya ce suna ajiye ba a taba su ba, duk da hakan wannan zaman bai bada damar kawo karshen rikicin ba.
‘Yan majalisun sun samu halartar zaman wanda aka yi shi ranar Alhamis da ta gabata a dakin taro na sakatariyar APC ta jiha, inad aka cimma yarjejeniyar yafe wa shugaban karamar hukumar zarge-zargen da ake masa tun da ya amsa laifinsa, tare da rubuta yarjejeniya inda duka bangarorin biyu suka sanya hannu har da su ‘yan majalisun. Sai dai LEADERSHIP A YAU ta fahimci zaman ya samu amincewar duka bangarorin a kan sulhun da aka yi, amma daga cikin kansiloli goma sha biyu da suka samu halartar zaman cikin sha uku da ke wakilci a karamar hukumar, kansiloli uku ba su gamsu da hukuncin kwamitin ba, don kuwa sun nuna rashin amincewarsu ga matakin da aka dauka.
Wakilinmu ya nakalto mana cewar, kansilolin sun bayyana cewar ba kansu suke wakilta ba jama’a ne suke wakilta kuma sakon da jama’a suka aiko su da shi, lallai a bari doka ta yi aikinta.
Bayan zaman sulhun, LEADERSHIP A YAU ta yi kokarin jin tabakin wadanda suka jagoranci wannan zama na Alhamis, wato ‘yan majalisar dokoki na jiha da na kasa a nan sakatariyar jam’iyyar APC din amma dukkansu sun ki su ce uffan kan lamarin.
A bangaren kansiloli kuwa da masu goyon bayan zaman da wadanda suka ki amincewa da hukuncin da aka yanke, babu wanda ya yarda ya ce wani abu game da lamarin, sai dai wani kansila daga cikin kasilolin ya ce za su nemi ‘yan jarida nan gaba kadan idon sun cimma matsaya da jama’arsu.
Da yake tattaunawa da manema labarai, wanda ake tuhumar kuma shugaban karamar hukumar ta Kontagora, Hon. Attahiru Ahmed ( Baban Makaranta) cewa ya yi, “Lallai na tafka kuskure, amma faruwar wannan lamari ba zai raba kaina da kansilolina ba zan tabbatar mun yi aiki tare kamar yadda dokokin kasa suka tsara”.
Ya kara da cewa, “Akwai yarjejeniya da muka yi a rubuce lallai za mu yi aiki kafada da kafada a kan wannan yarjejeniyar, a korafe-korafen da aka gabatar wasu sun faru, wasu kuma ba mu san da su ba, amma a matsayinka na babba komai ya taso sai ka runguma a wuce inda ake, mun yi kuskure kam amma za mu gyara”.