Zubairu M Lawal">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Na Dauki Matasan Jihar Nasarawa Kamar ’Ya’yana Ne – Silifat Sule

by Zubairu M Lawal
December 22, 2020
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Silifat Sule
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Uwar gidan Gwamnar jihar Nasarawa, Giwan Matan Nasarawa Hajiya Silifat Abdullahi Sule ta nuna goyon bayanta ga matasan jihar, a inda ta bayyana cewa ita Uwa ce a garesu, kuma duk wani goyon baya da ya kamata ta basu za su samu daga gareta.

Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke jawabi a wajen taron matasa da ya gudana a Filin wasa ta garin Gudi dake karamar Hukumar Akwanga cikin jihar Nasarawa.

samndaads

Taron da matasan garin Gudi suka shirya domin cigaban matasa da Kuma yankin Gudi.(Gudi Youth Progressibe and Debelopment Association).

Hajiya Silifat Abdullah Sule tace ita Uwa ce ga dukkanin matasan jihar Nasarawa kuma tana baiwa matasa tallafi a harkokin cigaba yadda ya kamata.

Hajiya Silifata ta ce tana alfahari da matasan jihar Nasarawa saboda yadda suke kokarin ganin cigaban jihar Nasarawa.

Hajiya Silifata ta kara kira ga Matasan jihar Nasarawa da su kara kaimi wajen tsayuwa da kafafun su domin cigaban jihar Nasarawa. Wajen kirkirar abubuwan cigaba da dogaro da sana’o’in hannu domin habbaka jihar Nasarawa a fannin tattalin arziki.

Uwargidan Gwamnan ta shawarci matasan jihar Nasarawa da su guji ta’amali da miyagun kwayoyi da harkon shaye-shaye saboda babu cigaba face jefa kai cikin hadari.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban kungiyar cigaban matasan garin Gudi Ezekiel Mathias ya bayyana Uwargidan Gwamna Hajiya Silifat Abdullah Sule da suna Maman Matasan Gudi.

Saboda duk gudumawa da kulawar da ya dace Uwa ta baiwa ya’yan ta Hajiya Silifat ta baiwa matasa.

Ya kara da cewa ya’yan kungiyar ( Gudi Youth Progressibe and Debelopment Association) ba zasu manta da Uwargidan Gwamnan ba saboda yadda take yaki da masu cin zarafin mata da yara kanana.

Ya ce , zuwan Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule tare da Hajiya Silifat mata da matasa sun amfana da tallafi na cigaba da harkokin Sana’a dabam dabam.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda NJC Ta Bada Shawarar Korar Babban Kadin Yobe Da Sauransu

Next Post

Ba Za Mu Sake Amincewa Da ‘Inconclusive’ Ba Ko Za A Mutu – Rabiu Kwankwaso

RelatedPosts

Ingantaccen zabe

Aniyar Ganduje Ce Ta Haifar Da Ingantaccen Zabe A Kano – Yusif Ali

by Zubairu M Lawal
2 days ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana cewa, kyakkyawar aniyar Gwamna...

Kaduna

Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Kwanton Bauna A Kaduna

by Zubairu M Lawal
2 days ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Sojojin da ke karkashin ‘Operation Thunder...

Farar Hula

Hankula Sun Tashi A Maiduguri Bayan Babbaka Sojan Da Ya Harbi Farar Hula Hudu

by Zubairu M Lawal
2 days ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mutanen Maiduguri sun shiga tararrabi bayan...

Next Post
Rabiu Kwankwaso

Ba Za Mu Sake Amincewa Da 'Inconclusive' Ba Ko Za A Mutu – Rabiu Kwankwaso

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version