Connect with us

NAZARI

Na Duke Tsohon Ciniki: ’Yan Nijeriya Mu Koma Gona

Published

on

Akwai gayar muhimmanci gwamnatoci su sake duba batun bunkasa harkokin noma a kasar nan, duba ga rawar da bangaren ke takawa a fannin ci gaban tattalin arzikin kasa, tare da samar da aikin yi ga miliyoyin matasa. Aikin noma ba kashin yasar wa bane ga duk kasar da tunaninta yake a jikin ta, a matsayin shi na ginshiki kuma babban kadarkon da zai iya jure kowace kwaramniyar ci gaban kasa tare da al’ummar ta baki daya.

Noma na duke tsohon ciniki; kowa ya zaka duniya kai ya tarar- wannan ko shakka babu, ta la’akari da dimbin albarkatun da yake kunshe dasu kuma masu dorewa, batukar akwai bil Adam a doron kasa, shi ne tushen duk wata hanya ko matakin ci gaban tattalin arzikin kowace kasar da ta shahara a duniya.

’Yan karin-magana sun ce: wanda ya tuna bara bai ji dadin bana ba, musamman ta la’akari da rawar da ayyukan noma su ka taka a Nijeriya a fannin ci gaban tattalin arziki, da tasirin noman gyada a arewacin Nijeriya ga tsarin tattalin arzikin kasar nan. Sananniyar tsibin dalar gyda a arewacin Nijeriya babbar alama ce kuma shaida ga kowa kan yadda mu ka tsere tsara kuma abin alfahari a shekarun da su ka gabata. Lamarin da ya kai mu ne kan gaba a tsakanin kasashen Afrika ta yamma, inda Nijeriya ce ke noma kaso 41 cikin dari na gyadar da ake nomawa a wadannan kasashen- daga arewacin kasar nan.

Haka kuma, idan mun kalli shekarar 1880, Allah ya albarkace mu da gonakin cocoa, a kudancin Nijeriya, musamman a Legas da Otta. Wanda har zuwa tsakanin 1950 zuwa 1970, Nijeriya ita ce ta biyu wajen noma cocoa a duk fadin duniya. Sannan ga gonakin noma kwakwar man ja a yankin kudu maso gabashin kasar nan, yanki ne wanda Allah ya yi masa tagomashin kwakwar man ja, bila adadin.

Bugu da kari kuma, baya ga arzikin albarkatun gyada, cocoa da kwakwar man ja, Allah ya sanya wa kasar mu albarkar noma itacen roba, auduga, ganyen taba da sauran kayan amfanin gona kala-kala. Wadanda dukan su masu kima ne a fannin bunkasar yanayin tattalin arziki, kana wadanda za su gina Nijeriya zuwa madaukakin matsayi da wakwala ga yan kasa.

A hannu guda kuma, wadannan kayan amfanin gona da Nijeriya ke samar wa, a kan duga-dugan su ne tsarin tattalin arzikin mu ke gudana tare da kasancewa madaukaka kuma aka san mu a tsakanin kasashen Afrika da ma duniya. Wanda sai a shekarar 1956, Nijeriya ta bude sabon shafin nasarar danyen man fetur, ta hanyar Oloibiri a jihar Bayelsa. Yayin da wannan shi ne soman tabin canja alkiblar inda kasar ta dosa a fannin tattalin arziki, kuma daga wannan lokacin ne fannin noma ya samu tazgaro da koma baya, gwamnatoci su ka karkata zuwa ga man fetur fiye da bayar da cikakkiyar kulawa ga ayyukan noma.

Bisa ga karkata akalar tattalin arziki daga sashen noma zuwa ga man fetur, ya jawo gagarumin sauyi, yayin da a tsakanin shekarun 1960 da 1970, ayyukan noma su ne kan gaba a fannin ci gaba da bunkasar yanayin tattalin arzikin Nijeriya- musamman gyda, wanda ake noma sama da ton miliyan 1.6. Amma a farkon shekarar 1980 adadin ya fado warwas, inda da jibin goshi ake iya noma gyadar da ta kai ton 700,000 kacal. Al’amarin da bai kyale noman Cocoa da dangogin su ba.

A wata kididdigar da hukumar kula da lafiyar dabbobi ta kasa (Federal Department of Libestock and Pest Control Serbice) ta bayar ya nuna yadda Nijeriya ke kan gaba a fannin kiwon dabbobi da tsuntsaye, wanda shi ne babban jigon bunkasar tattalin arzikin kowace kasa a duniyar nan. Yayin da wani bincike ya gano cewa, a 1990 Allah ya horewa Nijeriya shanu kimanin miliyan 13,947,000.

A cikin wannan adadin, jihar Borno ita kadai ta mallaki shanu kimanin miliyan uku, yayin da jihar Bauchi da tsohuwar jihar Gongola (Adamawa da Taraba yanzu), Kaduna, Nijar, Plateu da Sakkwato, kowanen su ya na da saniya (nagge) kimanin miliyan daya.

Haka zalika kuma, idan an koma gefen kiwon tumaki da awaki, jihohin Bauchi, Borno, da Kano, su na da tumaki da awaki sama da milyan biyu kowacen su, inda Katsina, Gongola, Sakkwato su na biye dasu da sama da miliyan daya kowacen su.

Jihohin Benuwai, Plateau su na kan gaba wajen kiwon akadai, inda a wancan lokacin kowacen su ta na da kimanin 500,000, sai Gongola da Kaduna na bin bayan su da 470,000 da 250,000. Haka zalika kuma, jihar Benuwai ce ke kan gaba wajen kiwon kaji (a wancan lokacin), inda take da kaji sama miliyan 8, sai jihohin Ogun, Oyo, Ondo, Anambara da Bendel ke bin bayanta da kaji sama da miliyan hudu kowacen su.

Bugu da kari kuma, a albarkatun kiwon dabbobin da tsuntsaye, jihohin Bendel da Benuwai su na kan gaba wajen kiwon agwagi sama da miliyan daya kowacen su, wanda Bauchi, Plateau, Gongola da Sakkwato ke biye da su da agwagin da su ka doshi miliyan daya kowacen su.

Har wala yau kuma, binciken ya nuna yadda jihohin Kano, Akwa-Ibom, da Plateau su ka zarta sauran jihohin kasar nan wajen kiwon talo-talo. Haka kuma, jihar Bauchi ta na kiwata zomaye sama da 500,000, idan an kwatamta da jihohin Kano, Katsina da Kaduna ma su yawan zumayen; 217, 166,000, da 112,000 a takaice.

Saboda haka, ya zama wajibi gwamnatocin Nijeriya su sake duba wannan lamarin wajen sake farfado da harkokin noma, wanda ko shakka babu zai kasance kan-da-garki tare da zama babban jigon ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, kamar yadda ya kasance a farko.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: