Na Fara Sana’ar Katako Daga Shekara Arba’in Zuwa Yanzu

Katako wani abu ne da ke da mahimmanci a rayuwar dan’adam, idan aka yi la’akari da yanda ake sarraafa shi na farko kafin ma ya zama katakon shi kansa ita cen  ana amfani da shi wajen girkin abinci kuma in an ga dama ana iya sarrafa sassakensa ko ganyensa ya zama maganin wasu cututtukan da ke jikin dan’adam karshe ma a sarra fa shi ya dawo katakon  nan shi ne ake sarrafa shi wajen rufe gidaje domin kare rayuwar da’adam sannnan kuma  ana iya sarrafa shi a yi kujeru da shi domin dan’adam ya zauna ya jidadin rayuwarsa kai da sauran abubuwa  da dama  da ake yi  da shi domin dan’adam ya amfani rayuwarsa a duniya haka ne ya sa wakilinmu na shiyyar Legas ya tambayi Alhaji Adamu wanda shi ne shugaba kasuwar sayar da katako na yankin Funtuwa game da wannan daraja da Allah ya yi wa icen da ake yanka shi ya zama katako.

Adamu ya ci gaba da cewa, lallai itace na da mahinmanci a fanin rayuwar dan’adam daban-daban. Haka kuma daga cikin  albarkar da Allah ya yi wa itace,ake samar da katako wanda ke taka muhimmiyar rawa a ci gaban rayuwar dan’adam. Saboda haka ya ce su ma irin wannan albarkacin suke ci, hart a kai ga sun mayar harkar sayar da katako ta zama hanyar da suke samun biyan bukatar rayuwarsu ta yau da kullum.

Exit mobile version