Abba Ibrahim Wada" />

Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Roland Koeman, ya bayyana cewa tuni ya fara lissafin yadda zai bullowa fafatawar da kungiyarsa za tayi da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German a wasan da zasu fafata na zakarun turai a wata mai zuwa.

A satin daya gabata ne Ronald Koeman, ya ce babu shakkah kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yi musu wanka da ruwan sanyi kuma ya bayyana gaskiyar halin da suke ciki na matsalolin da suka tilasta musu fuskantar kalubale a kakar wasan bana.
Koeman ya bayyana cewa duk da cewa an zura musu kwallaye hudu a raga amma duk da haka basu fitar da ran cewa zasu samu nasara ba akan kungiyar ta PSG idan an buga wasa na biyu a kasar Faransa kuma tuni ya fara tunani akan hakan.
“Duk da haka ina da kwarin gwiwar cewa zamu samu nasara a kansu a fafatawa ta gaba da zamuyi dasu saboda kwallo ce komai zai iya faruwa idan munje kasar Faransa buga wasa na biyu kuma ina fatan zamu samu nasara” in ji Koeman
Yayin wasan da suka fafata a satin daya gabata  dai matashin dan wasan kungiyar PSG, Kylian Mbappe ne ya nuna kansa inda ya ci kwallaye uku, ya yin da shima dan wasa Moise Kean ya ci kwallo daya, a bangaren Barcelona kuwa Messi ne ya ci mata kwallon guda daga bugun fanareti.
Sai dai kaftin din Barcelona Lionel Messi ya sha caccaka daga wasu magoya bayan kungiyar, da kuma masu sharhi kan kwallon kafa, dangane da gazawar da wasu ke ganin yayi wajen taimaka wa Barcelona ya yin wasan da PSG ta lallasa su da 4-1 har gida Camp Nou a gasar Zakarun Turai.
Tsohon dan wasan Chelsea Joe Cole ne na baya bayan nan da ya caccaki Messi, wanda ya ce alamu sun nuna cewa zuciyar kaftin din ba ta tare da kungiyar sa saboda gaba daya bai buga abinda akayi zaton zai buga ba.
Joe Cole ya kuma gargadi kociyan Manchester City Pep Guardiola da cewar, ya guji kulla yarjejeniya da Messi domin a cewarsa a halin yanzu kallon kitse ake yiwa rogo domin ba irin Messin da aka sani bane a shekarun baya.
A kakar wasan da ta gabata dangantaka tayi tsami tsakanin Messi da Barcelona, bayan da suka sha mummunan kayi a wasan gasar Zakarun Turan da Bayern Munich ta lallasa su da ci 8-2 a zagayen kusa dana kusa dana karshe.
A waccan lokacin dai Messi yayi yunkurin tilastawa Barcelona kyale shi ya sauya sheka kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyar sa da kungiyar, wadda a karkashinta yake da zabin rabuwa da ita a karshen kakar wasa, ko da kuwa wa’adin yarjejeniyar bai kare ba.
A halin yanzu kungiyoyin da ake alakanta Messi da su sun hada da kungiyar kwallon kafa ta PSG wadda ake ganin zaije ya hadu da tsohon abokinsa Neymar da kuma Manchester City wadda zai hadu da tsohon mai koyar dashi wato Pep Guardiola wadda kuma a shekarar bara suka soma tuntubar juna.

Exit mobile version