Na Fito Takarar Gwamnan Bauchi Ne Domin Ceto Jihar Daga Kisan Mummuke Da Ake Yi Mata (1) -Kaftin Bala Jibrin

KAFTIN MUHAMMAD BALA JIBRIN Daya ne daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamna a jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC, a hirarsa ta musamman da LEADERSHIP A Yau ya bayyana dalilan da suka sanya shi ke neman wannan kujerar. Kaftin wanda ya yi aiyuka daban-daban a jihar Bauchi ya kuma taba kasancewa shugaban karamar hukumar Katagum, gogaggen dan siyasa ne, ya shaida cewar ya fito neman gwamnan ne domin ceto jihar Bauchi. Wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi sun kuma tabo batutuwa da dama, ga hirar:

Da wa LEADERSHIP A Yau take tare?

Sunana Kaftin Muhammad Bala Jibrin dan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2019 da ke tafe.

Ka gabatar mana da dan takaitaccen tarihinka mana?

Suna na dai kamar yadda na shaida maka Muhammad Bala Jibrin an haifeni a karamar hukumar Azare a alif 1958, na yi Firamare dina da Sakandari dukka a garin na Azare, na zo na halarci kwalejin BAKAS da ke Bauchi da na kammala na tafiya jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na fara karatu daga nan kuma na zarce zuwa kasar Amurka inda na karanci koyon tuka jirgin sama na yi digiri na farko da na biyu dukka a Amurka a wannan fannin na tukin jirgin sama. Bayan da na kammala na zo na kuma je jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi karatun Lauya a shekara ta 2006 ne ka kammala.

Na yi aiyuka da dama, kadan daga ciki, na yi aikin tukin jirgin sama a kamfanin jiragen sama na ‘Nigerian Airways’ kuma na koyar da karatu a makarantar koyar da tukin jirgi da ke Zariya, sannan kuma na yi aiki a ma’aikatar sufurin jiragen sama a Abuja tun daga mataimakin Darakta har na zo na zama mai rikon Darakta a wannan ma’aikatar a bangaren kula da amincin zirga-zirgan jiragen sama da kuma kula da filayen jiragen sama a Nijeriya. da dai sauran aiyuka da na gudanar.

Sannan kuma a Bauchi an zabeni a matsayin zababben shugaban karamar hukumar Katagum a lokacin da aka yi siyasa a 1997-1998 kuma an nadani kwamishinan aiyuka, na kuma yi kwamishinan ilimi an kuma nada ni kwamishinan kimiyya da fasaha kuma na yi rikon kwamishinan watsa labarain na jihar Bauchi ka ji tarihina a takaice.

Wai shin takamaimai mene ne ya baka sha’awa ka tsunduma hidimar siyasa ne kam?

Ni na shiga siyasa ne tun a 1978 domin sha’awar da na ke da ita kan hidimar siyasa, na shiga jam’iyyar PRP a Samaru Zariya a lokacin ina dan makaranta a ABU, mune muka yi dan siyasar da ake kira ‘Bara’u’ wanda ya ci zaben sanata a karkashin PRP a wancan lokacin a yankin Zariya, mune muka yi gwagwarmayar siyasarsa tun daga kan kafa rumfunan kamfen da sauransu, mun sha hanu mun yi ido biyu da (Allah ya jikansa) marigayi Malam Aminu Kano, mun yi taro mun sha hanu da wanda ya ci zabe a nan jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa da sauran jiga-jigai a PRP a wancan lokacin.

A gida Azare ma dai, Allah ya jikansa shi ma yau baya nan, Alhaji Audu Nagado shi ma jigo ne a tafiyar jam’iyyarmu ta PRP a wancan lokacin. Bayan nan duk wata jam’iyya da aka yi kowace tun daga wancan lokacin za ka samu ni mamba ne dai a wata jam’iyya, a lokacin da aka yi guguwar NRC da SDP na shiga NRC, a lokacin da aka yi DPN da UNCP Santa Fati na shiga jam’iyyar DPN a nan ne ma na ci kujerar shugaban karamar hukumar Katagum. A lokacin da aka yi jam’iyyu na gaba da wadannan na ANPP-PDP-AD ni na shiga ANPP daga baya na koma CPC a lokacin maja da jam’iyyu na koma APC. Kada ka mance dukkanin jam’iyyun da na shiga sai ta kai na zama jigo a cikin tafiyar jam’iyyar na kasa.

A daidai wannan lokacin ka fito neman kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 wai shin mene ne ya sanya kake neman wannan kujerar?

Wato rashin iya shugabanci da rashin adalci da ake tafkawa a cikin gwamnatin da take ci a yanzu a wannan jihar ta Bauchi da kuma rashin samun wadanda suka fito suka kalubalanci ababen da ake yi ne ya sanya na zartar da cewar mu bamu da wata jihar da za mu je sai Bauchi, don haka ne na fito domin na ceto jihar Bauchi daga wannan mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki.

Wasu sun zo sun yi kaka-gida a jihar, sun karba suna yi suna kuma karyawa  da taka mutane, ana cin zarafin dattawa, saraukuna ana cin zarafin malamai na addinai, ana cin zarafin dalibai, dukkanin wani abu na kyautatawa ba a yi a jihar nan, an kawo mutane daga wasu wurare sune a cikin gwamnatin nan sune masu fada-a-ji.

Wai yau, yaro mai shekara 30 da dauri da ya zo daga wata jihar shine jama’a suke bin kafa ta hanunsa domin a basu shugaban karamar hukuma domin kawai yayansa na cikin gwamnati, wannan abun kunya ne, don me za a yi mana haka? Ta ina ne muka gaza a jihar nan? a jihar Bauchi ne fa a da baya ake zuwa koyon aiki, an san mutanen Bauchi da ilimi, an san mutanen Bauchi da daidaita al’amura, amma yau a ce  a jihar Bauchi wani ya zo ya sanya mu a gaba, an yi shiri an sanya masa ido, ya ci mutuncin kowa ya taka kowa, ya yi karya a cikin mutane ne, ya yi yaudara a cikin mutane, ya fadi abun da ba a taba yi ba, to wadannan ababen suna daga cikin dalilan da suka sanya na ga  dole ne mutane masu mutunci su zo, mutanen da suka dace su yi jagoranci dole ne su zo su yi, wannan dalilai suna daga cikin abun da ya kawoni neman gwamnan jihar Bauchi.

Wasu manufofi ko buri ka ke da su wa jihar Bauchi?

Da farko burina na farko shine a fara daidaito da al’amura, akwai ababe da daman gaske da aka lalatasu da gangan aka batasu don son rai da son zuciya, sannan zan dawo da martabar aiki, a dawo aiki yadda aka san aiki, dan kwangila ya san shi dan kwangila ne domin ya san yadda zai gudanar da aikinsa na kwangila, ma’aikaci ya san shi ma’aikaci ne ya gudanar da aikinsa a matsayinsa na ma’aikaci, ba wai Baba na Daka gemu na waje ba; kana gwamnati kana kwangila, ka kawo ‘ya’yanka, ka kawo matanka, ka kawo ‘ya’yan ‘yan uwan matanka, ka kawo abokanka, kun zo kune gwamnatin kune ‘yan kwangilan kuma kune masu biya. Wannan abun ba za a ci gaba da yinsa ba, idan na samu nasara, dan kwangila ya tsaya matsayinsa, haka shi ma ma’aikaci ya tsaya a matsayinsa, kowa ya yi aikinsa ya taka rawarsa domin ci gaban jihar, amma a ce mutum daya shine mai gudanar da komai wannan ba daidai ba ne ba kuma za mu amince da hakan ba. sannan kuma zan yi garan bawul wa sha’anin ilimi, tabarbarewar sha’anin ilimi ya fi komai illa. ga kuma rashin tarbiyya na yara da ake fama da shi; an yi murna a da kwanta-kwanta ta kare, sara-suka ta kare, amma a ‘yan kwanakin nan sai ga sara-suka ya dawo, domin mutum don ba ‘ya’yansa ba ne, ba ‘ya’yan kawonansa ba ne, ba ‘ya’yan Baffani ko kakakinsa ba ne, aka sanya yara su koma sara-suka. Kowa ya sani an sari Haruna Ningi, shi wannan Haruna Ningi koda a waka ya tsaya ai shi jakada ne babba na jihar Bauchi a fannin wake, tun da ba sata yake yi ba, ba kuma shaye-shaye yake yi ba, waka ne sana’arsa, wakokin da ya yi wa jam’iyyar da ba tawa ba, sun zama bakandami wa ita wannan jam’iyyar, kuma dan jihar Bauchi ne, don haka yana da girma ko yau aka ce Haruna Aliyu Ningi dan jihar Bauchi ne da Ningi ake kiransa, ka je ka sa an sareshi, an je kotu an yi awa biyu an sake wadanda suka saresu, a labarin da muka ji akwai hanun wasu lauyoyin gwamnati domin sun shiga cikin lamarin.

Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa

 

 

Exit mobile version