El-Zaharadeen Umar" />

Na Fito Takarar Majalisa Ne Don Habbaka Rayuwar Mata –Halima Shata

Daya daga cikin ‘ya’yan shahararen mawakin arewacin kasar nan, Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, Hajiya Halima Mamman Shata ta bayyana sha’awarta ta tsayawa takarar ‘yar majalisar dokoki ta jihar Katsina, Mai wakiltar karamar Hukumar Funtua a zauren majalisar dokokin a kakar zabe mai zuwa ta 2019,.

Da take karin haske dangane dalilai da yasa ta fito takarar, a tattaunawarta da LEADERSHIP A Yau inda ta ce “na fito domin in bada gudunmuwa ga cigaba karamar Hukumar Funtua da kawo kudurorin da za su kawo cigaban matan da inganta rayuwar su a jihar Katsina da kasa baki daya’’.

Halima Shata ta kara da cewa mata Suna da rawar da za su taka, a harkar siyasa amma sun yi barci an bar su a baya musamman a arewacin Nijeriya, inda zaka ga kalilan ne ke fitowa takara, saboda wadansu dalilai. Kuma su mata sune suka fi fitowa a ranar zabe, kuma kullum sune ake bari a baya. Idan Allah ya bata nasara zata tabbatar da an yi dokoki da za su inganta rayuwar matan jihar Katsina da kuma karfafa rayuwar su.

‘Yar takara ta cigaba da cewa “Kodayaushe Ina kara samun kwarin gwiwa a harkar siyasa saboda Mahaifinmu dan siyasa ne, amma ni na ta so na ga yana harkokin siyasa wadda har ya taba zama shugaban jam’iyya da kuma takarar shugabanci kasar nan kuma cikin ‘ya ‘yansa ina alfahari da na gajeshi bangaren siyasa, kuma zan cigaba da jajircewa domin ita ce matakin nasara’’.

Daga karshe, Hajiya Halima Mamman Shata Katsina ta yabawa Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari saboda irin goyan baya da kwarin gwiwar da yake nunawa da yin kira mata su fito a dama da su a harkokin siyasar jihar Katsina.

‘’Kuma ina jinjina ma shi irin cigaban da jihar Katsina ta samu karkashin jagorancin sa musamman a fannin lafiya, ilimi da kuma koyawa mata sana’o’i da Samar da tsaro’’. In ji ta

 

Exit mobile version