Mustapha Ibrahim" />

Na Fuskanci Babban Kalubale Lokacin Da Na Kafa Masana’antar ASAD – Ahmad Danbaba

Ahmad Danbaba

Daya daga cikin Mutane masu taimakawa a karamar hukumar Dawakin Tofa ko ma Masarautar Bichi bakidaya, Alhaji Ahmad  Sunusi Danbaba, ya bayyana cewa, ya fuskanci kalubale mai yawa a lokacin da ya kafa masana’antar sarrafa Sabulu irinta ta farko a masarautar Bichi domin kuwa bayan kafa wannan masana’anta wanda sai da ya dau matasa sama da 200 ya horar ya kuma koya musu wannan sana’a da ya koyo a yawan shin a kasashin Duniya kuma ya dau matasa sama da 20 a karan farko na bude masana’antar to amma ya fuskanci kalubale mai tarin yawa daga hukumomi daban daban wanda bacin hakuri da dauriya da al’umma bata ci gajiyar wannan Masana’anta ta ASAD a yanzu ba.

Alhaji Ahmad ya kara da cewa budewar sa wannan Masana’anta ked a wuya sai hukumomi masu ruwa da tsaki a kan irin wannan sana’a su kai ca a kansa, wanda sai da ya rufe wannan masana’anta kimanin shekara Guda domin shige da fuce na ga ya bi sharadan hukumomi irin su NAFDAC hukumomin Lafiya da sauran hukumomi, wanda ma wasu ba su da alaka da wannan aiki amma dai haka yaci karo da irin wannan matsaloli na kalubale kuma ya daure wanda yanzu haka akwai masa dad a 30 da su ke aiki a wannan masana’anta ta ASAD ban da wadanda su ke cin gajiyar wannan masana’anta sakamakon aikinta, don haka akwai bukatar al’umma su rika jajircewa da dauriya wajen cimma Nasarar abunda suka sa gaba komai kalubalan da ke ciki.

Haka zalika ya ce wani abun sha’awa shi ne duk da kasancewar injinan sun samo asalin ne daga Turai amma shi injinan da ya ke sarrraafawa shiya zana su kuma shiyasa a haka kerasu a gabansa kuma da su ya ke aiki a yanzu dan haka wannan ma babbar nasara ce a gare shi da sauran Al’umma.

A karshe ya kira da daukacin hukumomin Jaha dana tarayya da kuma iyayan mu Sarakuna akan su rika tsayawa tsayin daka kamar yadda suka gada daga iyayen su da kakan nun su na aga Al’umma ta cigaba musamman ta hanyar amfani da irin wadannan kayayyaki na Gida wanda zasu taimaka wajan daukar matasa aikin yi wanda zai bukasa tattalin Arziki da kuma rage zaman banza ga matasa a ko ina a ko da yaushe  inda kuma ya yabawa Gwamnan kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje kan kokarin da ya ke yi wajan cigaban zaman Lafiya a Jahar kano kasancewar zaman Lafiyar shi ne kashin bayan cigaban Al’umma da kuma fatan Alkairi ga Mai Martaba Sarkin Bichi  Alhaji Aminu Ado Bayero da Hakimai da Dagatai da Masarautu Biyar da sauran Al’ummar kano da kasa baki daya.

 

Exit mobile version