Zakaran damben duniya dan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, ya bayyana cewa shima ya gama shiryawa domin fafata wasa da Tyson Fury, dan burtaniya, a wasan da zakarun biyu zasu kece a sabuwar shekara mai zuwa.
A kwanakin baya ne shahararren dan wasan Dambe na duniya Tyson Fury ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fafata wasan Dambe da zakaran wannan lokacin Anthony Joshua a wasan da ake saran za’a fafata a shekara mai zuwa a birnin Landan din Ingila.
Tyson Fury, wanda shima ya shahara a duniya a fannin dambe ya ce cikin zagaye na uku gaba daya zai doke Joshua saboda shi har yanzu ba sa’ansa bane kuma yana da kwarin guiwar samun nasara akan matashin dan asalin Nijeriya.
A tsakiyar wannan watan ne dan damben Burtaniya Anthony Joshua ya doke Kubrat Puleb, dan asalin kasar Bulgeria wanda hakan ya kara fitowa da batun karawarsa da Tyson Fury fili kuma Joshua ya yi nasara ne a fafatawar da aka kai zagaye uku ana yi.
Furta hakan ke da wahala kuwa sai Anthony Joshua ya ba su amsar cewa ‘duk wanda ke da tarin kofuna ya zo na shirya’ kuma idan ma Tyson Fury ne, to shi ke nan a shirye yake ya kara da Tyson Fury’.
Ba da wata wata ba kuwa sai shima Tyson Fury ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ‘to kun ji amsar Anthony Joshua game da karawa da ni kuma nima na shirya, na matsu na doke shi’ cikin zagaye uku kacal”.
‘Yan kallo 1,000 ne aka baiwa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bada tazara saboda annobar Korona sai dain idan ba’a manta ba kadan ya rage ganiyar Joshua ta ruguje a watan Disambar bara, a lokacin da ya dauki fansa kan Andy Ruiz Jr.
Kuma kisan da ya yi wa Kubrat Puleb a daren Asabar ya nuna cewa a yanzu Tyson Fury ne kawai ya rage su saka zare, don ya tabbatar wa duniya kololuwar inda kwarewarsa ta kai a duniyar dambe.
Anthony Joshua Murdadde ne na kin karawa, hannayensa cike suke da damatsa, sannan yana magana da murya mai sanyi, hade da murmushi a fuskarsa sannan a fagen dambe, yana da tarihin yiwa abokan karawarsa kwaf daya, yana da sunaye iri-iri na jarumta, abin da ke nufin cewa ga mutane da dama, Joshua ne gagarabadau cikin yan damben da suka fito daga Najeriya tun bayan gwarzon NBA Hakeem Olajuwon.
Tuni Joshua ya fara shafar rayuwar samari da yawa musamman a kudu maso yammacin Najeriya, kamar Legas babban birnin kasuwancin kasar domin da yawa daga cikinsu sun kalli yadda ya zama shahararre ya cika burinsa na rayuwa, kuma labarinsa kusan yazo dai-dai da nasu, na wanda ya sha wahalar rayuwa kafin daga bisani kofar arzikinsa ta bude ya sha kwana.
Labarinsa, wani abu ne da aka jima ana nuna irinsa a fina-finai irin na Nollywood, kamar dai ace na mutumin da burinsa na rayuwa ya cika bayan shan kwarba shekara da shekaru sannan Joshua ya zama wata sila ta samun karbuwar harkar dambe a Najeriya, domin a yanzu, har ta kai ga ana horar da mutane wasan a makarantu bayan tashi daga karatu, da kuma ranakun hutu da sauran wurare da dama.