Gernot Rohr ya ce an bai wa kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nigeriya Ahmed Musa gurbin girmamawa na musamman a tawagar Najeriya da za ta kara da kasashen Benin da Lesotho a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar Kamaru zata karbi bakunci..
Super Eagles za ta buga wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasashen biyu cikin watan Maris, domin zuwa gasar da Kamaru za ta karbi bakunci, gasar da akayi niyyar bugawa a wannan shekarar amma annobar cutar Korona tasa aka dage zuwa shekara mai zuwa.
Bayan da aka bayyana sunan Ahmed Musa, cikin tawagar Najeriya, hakan ya sa ake cece kuce kan dan kwallon da ba shi da yarjejeniya da wata kungiya tun cikin watan Oktoba da ya bar kungiyar Al Nassr ta Saudi Arabia.
Hakan ne ya sa Rohr ya fayyace rawar da Musa mai shekara 28 zai taka a Super Eagles a wasanni biyu da za ta kara bayan yasha korafi daga bangarori da daman a kasar nan akan kiran dan wasan da bashi da kungiya.
”Musa zai taka rawar gani a cikin ‘yan wasan da muka gayyata a fafatawar da za muyi da Benin da kuma Lesotho a wasannin neman zuwa kofin nahiyar Afirka kuma mun gayyace shi a matakin kyaftin kuma shi ne na 24, amma ba zai buga wasannin da zamu yi ba”. In ji Rohr
Sai dai ba a gayyaci tsohon dan wasan Manchester United Odion Ighalo ba wanda ke buga wasa a kasar Saudi Arabia, wanda Rohr ke kiransa da ya dawo bugawa Nijeriya wasa, bayan ritaya da ya yi.
Nigeria za ta ziyarci kasar Benin ranar 22 ga watan Maris a wasan daga karshe ta karbi bakuncin tawagar ‘yan wasan kasar Lesotho ranar 30 ga watan Maris, a jihar Legas kuma shi ne wasa na karshe a cikin rukuni.
Najeriya wadda ta lashe kofin nahiyar Afirka karo uku ita ce ta daya a rukuni na 12 da maki takwas, sai kuma kasar Benin mai maki bakwai, sannan kuma sai Saliyo da maki uku da kuma Lesotho mai maki biyu.
Tawagar Super Eagles da aka gayyata:
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (APOEL Nicosia, Cyprus) da John Noble (Enyimba FC) da kuma Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)
Masu tsaron baya: Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain) da Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland) da Chidozie Awaziem (Boabista, Portugal) da William Troost-Ekong (Watford, England) da Olaoluwa Aina (Fulham FC, England) da Jamilu Collins (SC Padeborn, Germany) da Zaidu Sanusi (Porto, Portugal) da kuma Tyronne Ebuehi (Twente, The Netherlands).
Masu buga tsakiya: Oghenekaro Etebo (Galatasaray, Turkey) da Wilfred Ndidi (Leicester City, England) da Abdullahi Shehu (Omonia Nicosa, Cyprus) da Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland) da kuma Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England).
Masu cin kwallaye: Aled Iwobi (Eberton, England) da Sadik Umar (Almeria, Spain) da Samuel Chukwueze (billarreal, Spain) da bictor Osimhen (Napoli, Italy) da Kelechi Iheanacho (Leicester City, England) da Samuel Kalu (Girondins Bordeaud, France) da kuma Moses Simon (Nantes, France).
Gurbi na musamman: Ahmed Musa
Masu jiran ko ta kwana: Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa) da Henry Onyekuru (Galatasaray, Turkey) da Peter Olayinka (Slabia Praha, Czech Republic) da Terem Moffi (Lorient, France) da Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium) da Michael Olise (Reading, England) da kuma Adekunle Adeleke (Abia Warriors).
Leceister City Ta Je Wasan Karshe A Kofin FA Bayan Shekara 52
Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta kai wasan karshe...