Shafin RUMBUN NISHADI, shafi ne da ya saba zakulo muku manyan jarumai har ma da kanana daga cikin masana’antar Kannywood. A yau ma shafin na tafe da daya daga cikin masu shirya finafinan hausa kuma mai taka rawa a cikin masana’antar Kannywood, wato USMAN ABBAS MUHAMMAD ALI wanda aka fi sani da DAN’DUNIYA.
Inda ya bayyanawa masu karatu irin gwagwarmayar da ya fuskanta yayin shiga masana’antar kannywood, har ma da irin nasarorin da ya samu.
- ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Jerin Ayyuka Karo Na Uku A Wajen Kumbon
- Hanyoyi Goma Sha Daya Da Mace Za Ta Bi Domin Janyo Hankalin Mijinta
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar LEADERSHIP Hausa RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko za ka fara fadawa masu karatu cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi?
Ni sunana Usman Abbas Muhammad Ali, a yanzu ana kira na da Dan’duniya.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Asalina ni mutumin Sudan ne, kuma haifaffen Sudan, yara na ma duk a can na haife su, a can na yi aure, na yi karatu, na yi komai a Sudan. Asalin Mamana da Babana Sudan ne.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Abin da ya sa na shiga ina sha’awar aikin, kuma ina jin dadin abubuwan da suke yi. Saboda a yadda na gani na dauki aikin fadakarwa ne, da jan hankalin matasa to, kuma ina sha’awar abun tun da dadewa. Dan na so na shiga harkar tun da dadewa Allah bai yi ba, sai a wannan lokacin.
Wane rawa ka ke takawa a cikin masana’atar Kannywood?
Ina taka rawa matsayin jarumi, kuma ina shirya fim wato aktin da kuma furodusin. Sai dai har yanzu ban saki finafinan dana shirya da kaina ba, amma akwai wanda in sha Allahu nake dab da sakinsa cikin wannan wata, fim din shi ne; GIDAN DUNIYA.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Gaskiya na sha wahala bayan na shiga masana’antar Kannywood, na hadu da azzalumai da macuta da mayaudara. Na yi ma wani fim me suna ‘Sama’ila Dillali’ to, karshe ma aka cinye fim din gabadaya ban san inda yake ba. Ba kudin babu sakin fim din, ba a yi komai ba, karshe ma aka ce an sace fim din gabadaya. To, kuma gaskiya an karbi kudade na da yawa a kan za a saka ni, ko kuma za a yi min kuma ba a yi ba. An yaudare ni sosai, gaskiya Alhamdulillahi yanzu dai na waye na san me nake yi.
Ko akwai wani mataki da ka dauka game da abin da aka yi maka?
Gaskiya ban dauki wani mataki ba, daga karshe ma sai na ji dadin faruwar hakan. Saboda dana fahimci hakan sai na ga karin wayewa ne da kara sanin me zan yi gaba?, da wa zan yi mu’amula a gaba?. Amma a farko na ji haushi, yanzu kuma sai na ga abun ai gara ma da ya faru, saboda yanzu na san da wanda zan zauna, kuma na san da wa zan yi hulda, na san kuma yadda zan yi na zauna da mutane.
Idan na fahimce ka daidai, lokacin da za ka fara shiga harkar, ka je ne ba tare da sanin kowa ba, ko kuwa akwai wanda ka sani, amma duk da haka aka yi maka hakan?
Eh! Gaskiya ne, lokacin dana shiga masana’antar, na je ne ba tare da sanin kowa ba kuma babu wanda ya kai ni, asalima na gansu suna shutin ne a unguwar mu. Mai dakina mata ta ce ta fara gano su, sai ta zo ta sanar da ni, sai na tashi na je wajensu nayi magana. Wanda na fara samu a lokacin Nura Dan’dole wanda ake kira da Yaya Dan’kwambo, na yi masa magana sai ya nuna min wanda zan yi wa magana ya ce su ne furodusa ga darakta, ni ma aiki aka kawo ni. Shi ne na yi musu magana suka kai ni kamfani na Kairiyya, suka hada ni da wani ana kiransa da Shugaba, Murtala Abdullahi kenan. Bayan hakan a nan ne na samu wani wanda shi ne ya yaudare ni, bayan ya zo ‘meeting’, suna yin ‘meeting’ duk ranar juma’a, sai ya dauki Lambata ya kira ni cewa, akwai wani aiki da za mu yi, idan za ka iya daukar mauyinsa, ka yi aikin ka ga aiki ne me kyau, sai muka je muka soma aikin tare da shi, wannan shi ne wanda ya yaudare ni.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?
Ban wuce shekara biyu ba.
Ya farkon fara dora maka ‘camera’ ya kasance?
Farko duk wanda ya ganni a lokacin zai ce kamar daman na saba, ko daman na iya. Saboda a yadda na zo kuma a yadda na shiga, ba wanda ya yi zaton ma ban taba yi ba. Abu guda ne aka gyara min, aka ce na daina kallon ‘camera’. Sai na biyu wanda aka ce “Ka daina hada ‘dialogue’ in wannan na magana, ka bari sai ya sauke shi, kai ma sai ka yi”. Tunda aka gyara min a sau daya wadannan biyun, ba a sake yi min gyara ba.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta daga gida, game da harkar fim din da ka fara a lokacin?
Gaskiya babu wani kalubale dana fuskanta, mahaifiyata tunda na fada mata ga abin da nake ciki, sai ta yi min addu’a ta ce; “To, Allah ubangiji ya sa a gama lafiya, kuma a rike amana, a rika sallah a kan lokaci.
Ka fito a finafinai, sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya ban sani ba, suna da dan yawa, ba wani sosai ba, amma ba zan iya tantancewa ba ko fim nawa nayi.
Wane irin nasarori ka samu game da fim?
Nasarar da na samu ba ta wuce jaruman da nake haduwa da su ba manya maza da mata, wanda suke nuna min soyayya da kowane lokaci na hadu da mutum aka ce jarumi ne sai ya nuna yana sona, sannan ya nuna kamar daman ya sanni. Haka kuma ban taba haduwa da wani jarumi, ko jaruma da ta wulakanta ni ba. Dan haka ina godiya ga Allah subhnahu wata’ala dan wannan wata nasara ce.
Wane abu ne ya fi wahala tsakanin shirya fim, da kuma fitowa matsayin jarumi?
Ni dai shirya fim ya fi wahala a wurina, kowa da abin da yake yi kasa sauki da kuma wahala, ni dai aktin baya ba ni wahala, kowanne irin ‘acting’ ne.
Kamar wadanne abubuwa ne suka fi wahala wajen shirya fim?
Abin da yake ba ni wahala shi ne, wajen hada kan jarumai, dan jarumai su ne fim idan babu jarumai babu fim, hada kansu shi ne me wahala. Saboda za ka iya hada komai da komai ka biya, amma kuma kafin ka hada jaruman da za ka yi aikin da su shi ne babban matsala.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta wajen wani jarumi ya yin shirya fim?
Gaskiya ban taba fuskantan wani kalubale ba, asalima muna girmama juna.
Ya ka dauki fim a wajenka?
Na dauki fim sana’a, idan ka rike ta za ka tsira da mutuncinka, kuma basira ce, mutumin da ba shi da kwakwalwa da tunani ba zai iya yin ma fim din ba.
Kafin ka fara fim wadanne jarumai ne suke burge ka?
Akwai Adam A. Zango, Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Daushe, Bosho, duk suna burge ni. A mata kuma akwai mamata wacce take uwa ce gare ni har yanzu, Hajiya Adaman Kamaye. Sannan akwai Haj. Ladidi Fagge, Haj. Zulai Bebeji, duk kaninsu aktin dinsu yana burge ni. A matasa kuma kamar yara-yara akwai Abbale, Dan’auta da ‘Yar’auta, akwai Ayatullahi duk da cewa har yanzu da nake masana’antar ba mu taba haduwa da shi ba, amma yana burge ni, tun a ‘da’ har yanzu.
Wadanne jarumai ne baka yi fim da su ba, cikin jaruman da suke burge ka?
Gaskiya suna da yawa.
Ya ka ke kallon irin maganganun da ake yi marasa kyau game da jaruman kannywood?
Gaskiya wannan maganganun suna bata min rai, ko maganganun da ake yi a kan social media walau matansu walau mazansu abun na batan rai. Saboda duk ana yin su ne dan neman ‘followers’ ba wani abu ba, ko a kafe hoton mutum ace ya mutu, ko a kafe hoton wata ace ta yi abin da bai kamata ba a fada duk dai an bata mata suna, kuma ana yinsa ne dan neman mabiya, abun na batan rai.
Bayan fim kana wata sana’ar?
Ina sana’a, ina tafiye-tafiye, ina zuwa kasar larabawa kamar irin; Dubai, Egypt, Turkiya, Yammel, Saudiya. Yanzu ma ban wuce kwanaki ba da zuwa, ina sana’a sosai.
Ya ka ke iya hada tafiye-tafiyenka, da kuma sana’ar fim?
Haka dai ake yi, a yi kasuwancin a yi tafiye-tafiye, lokacin da ake da aikin a yi. Shi aikin fim ba kowane lokaci yake samuwa ba, in ya samu za ka yi, kuma tafiye-tafiyena ba dadewa nake yi ba bana wuce wata daya ko sati biyu nake dawowa.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Burina na ga sunana ya daukaka, ko’ina an sanni. Shi ne kawai burina, ban da wani buri.
Me za ka ce da masu kallo?
Su ci gaba da kasancewa tare da mu, in sha Allahu muna nan za mu kawo musu finafinai masu kayatarwa, dan akwai wanda muke aikinsa yana kan hanyar fita mai suna GIDAN DUNIYA, fim ne wanda ya hadar da komai da komai, fadakarwa, nishadantarwa, wa’azantarwa in sha Allahu zai burge masu kallo. Sannan su ci gaba da yi mana uzuri, dan’adam tara yake bai cika goma ba.
Wacce shawara za ka bawa masu kokarin shiga harkar fim har ma da wadanda ke ciki?
Su rike sana’a, mutum ya san yana da sana’a, kar ya dogara ga fim shikkenan, saboda ba kodayaushe ake samun aikin fim ba.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Akwai iyayena mata da maza wanda suke a masana’antar kannywood, Hajiya Adaman Kamaye, Haj. Ladidi, Haj. Zulai. Maza akwai; Malam Hussaini Sule Koki, akwai maigidana Adam A. Zango, Ali Nuhu, Sani Danja, Sadik Sani Sadik, da sauransu. Ina yi musu gaisuwa da fatan alkhairi.
Muna godiya da ba mu lokacinka da ka yi
Ni ma na gode, Allah ya sa albarka, ubangiji Allah ya kare ku daga sharri da bala’i, Allah ya rufa muku asiri, Allah ya kiyaye.