Isa Abdullahi Gidan Bakko" />

Na Hari Mai-Allah Ya Zama Shugaban Kafintocin Sabon Garin Zariya

Hari Mai-Allah

Exif_JPEG_420

A ranar Asabar da ta gabata, daukacin ma su sana’ar kafintoci a kasuwar ‘yan katako da suke Sabon garin Zariya suka gudanar da sabon zaben sabbin shugabannin kungiyar da za su shugabanci kungiyar nan da shekara hudu ma su zuwa.

Wani abin sha’awa da ya faru a wajen wannan zabe da aka shafe kimanin sa’o’I takwas, daukacin kafintoci manya da kuma kanana sun halarci wajen zaben da ya gudana a tsakiyar kasuwar ‘yan katako ya gudana acikin lumana tare da bin dokoki da tsare – tsaren da wadanda suka tsara gudanar da zaben suka tsara domin zaben sabbin shugabannin.

A gefe guda kuma a kan al’amarin da ya shafi tsaro kuma babu ko shakka, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda na ofishin rundunar ‘yan sanda na hukumar jiragen kasa da ke Zariya da kuma jami’an tsaro da suke karkashin wannan kungiya ta kafintoci, sun bayar da duk gudunmuwar tsaron da ya dace na ganin an fara wannan taro lafiya, an kuma kammala lafiya.

Alhaji Suleiman Ishak shi ne babban jami’in da ya gudanar da zaben, shi ma a lokacin da ya tashi domin bayyana sakamakon zaben, da farko sai da ya nuna matukar jin dadinsa da kuma yabo ga daukacin ‘ya’yan kungiyar kafintoci musamman wadanda suke da katin zabe na hyadda suka bayar da duk goyon baya da bin dokokin da aka tsara domin gudanar da wannan zabe na kujerun da kungiyar ta tsara a cikin kundin ta.

Alhaji Suleiman ya ci gaba da cewar, a lokacin zaben sun yi zabe a kujeru guda goma babban jami’in tsaro na kungiyar [ PROBOST ] da jami’in watsa labarai da jagoran matasa da jami’in jin dadi da walwala na kungiyar da sakataren shirye – shirye da sakataren kudi da ma’aji da mai binciken lalitar kungiyar da babban sakataren kungiyar da babban ma’aji da kuma babban shugaban kungiyar ta kafintoci.

Bayan ya bayyana sakamakon zaben Alhaji Suleiman Ishak ya ya yi kira ga wadanda ba su sami nasara ba, da su hada hannu da wadanda suka sami nasara, domin ci gaban kungiyar da kuma mambobin kungiyar baki daya, ga wadanda suka sami nasara kuma, a nan sai ya tunatar da su cewar, ba wayonsu ya zama silar nasarar da suka samu ba, a cewarsa, Allah haka ya tsara cewar, za a yi wannan zabe, su ne za su sami nasara, sai ya ce, wajibi ne su nemi wadanda ba su sami nasara ba, domin su hada hannu wajen gudanar da ayyukan da za su ciyar da wannan kungiya da mambobin kungiyar gaba.

A dai jawabinsa ya jinjina wa shugabannin da suka gabata na wannan kungiya, bisa jagorancin Alhaji Ahmed Isa Gora, na yadda a lokacinsa, kamar yadda Alhaji Ishak ya ce sun aiwatr da ayyuka da dama da suka ciyar da kungiyar da mambobin gaba a wannan sana’ar da suke yi ta kafinta, sai ya shawarci tsofaffin shugabannin da su ci gaba das a sababbin shugabannin a kan hanya, ta yadda za su gane bakin zaren shugabancin da za su fara, domin a karshen shugabancinsu, a yi tozali da ayyukan ci gaba da suka a iawatar nan da shekara hudu ma su zuwa.

Alhaji Mohammed Salisu Auta, uba ne a wannan ku giya gta kafintoci, da farko nuna matukar jin dadinsa ya yin a yadda aka hyi zaben lafiya, aka kuma kammala lafiya, musamman a cewarsa in an dubi yadda al’umma suka fito da karfinsu domin neman shugabancin wannan kungiya daga lokacin da aka sa ranar zaben ya zuwa ranar da aka kammala zaben.

Alhaji Auta ya ci gaba da cewar, yadda aka gudanar da zaben, ya ce dole ya jinjina wa wadanda suka jagorancin zaben, na yadda suka yi tsare – tsaren day a haifar da zaman lafiya daga fara shirye – shiryen ya zuwa kammala zabubbukan da aka yi, sai ya yi kira ga wadanda suka sami nasara da su gode wa mai duka, na yadda ya ba su nasara, ba domin iyawarsu ba, ga wadanda suka kasance a tarragon rashin nasara, sai bukace su da su mayar wukarsu a cikin kube, ‘’ ku rungumi sabbin shugabannin da Allah ya ba su nasara, domin ci gaban sana’ar kafinta da ci gaban kungiyar baki daya.

Alhaji Suleiman Yusuf Na Hari Mai Allah, shi ne wanda Allah ya ba shi nasarar zama shugabancin wannan kungiya, ya fara da bayyana yadda aka gudanar da zaben inda ya nuna matukar gamsuwarsa da yadda aka yi zaben a cikin tsari mai inganci da babu wani dan takara day a koka da tsare – tsaren da wadanda aka dora ma su alhakin suka, y ace dole ya jinjina wa shugabannin da suka yi zaben ya zuwa bayyana wadanda suka sami nasara.

Da kuma ya juya ga wadanda ba su sami nasara ba, a nan sai ya yi kira a garesu da su amsa kirarsa na su kasance ma su bayar da duk gudunmuwar da suka dace, domin, domin ci gaban kungiyar da ‘ya’yan kungiyar baki daya.

Har’ila yau, Na Hari mai Allah ya yaba wa tsofaffin shugaban day a gaje su, na ayyuka tukuru da suka yi, na yadda suka sami samar da nasarori ma su yawan gaske a tsawon lokacin shugabancin da suka yi a wannan kungiya..

Bayan kammala zaben tsohon shugaban kungiyar Alhaji Ahmed Isa Gora ya nuna matukar jin dadinsa na yadda ya fara shugabancin kungiyar cikin kwanciyar hankali ya kammala lafiya, ya ce ya na shirye ako wane lokaci, ya ba sabbin shugabannin duk gudunmuwar shawarwari da suke bukata, domin gane bakin zaren da za su ja, domin ci gaban kungiyar baki daya.

A karshen zaben, Alhaji Ibrahim Datti da kuma Alhaji Ummaru shugaban matasa na kungiyar ‘yan kasuwar sabon garin Zariya, da suka wakilci Shugaban ‘yan kasuwar Sabon gari Alhaji Ibrahim Mai gwal, sun yaba da yadda aka gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali, sai suka yi kira ga sabbin shugabannin das u rike amanar da aka damka ma sun a shugabancin wannan kungiyar kamar yadda tsohon shugaban kungiyar Alhaji Ahmed Isa Gora ya yi.

Exit mobile version