Connect with us

MANYAN LABARAI

Na Ja Kunnen Kwankwaso Kar Ya Ba Ganduje Takara –Kawu Sumaila

Published

on

Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar tarayya Honarabul Kawu Sumaila, ya bayyana cewar ya gargadi tsohon gwamnan jihar Kano, Ininiya Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya tsayar da mataimakinsa Dakta Abdullahi Umar Ganduje takara.

A hirarsa da PREMIUM TIMES Kawu Sumaila ya ce shi da kan sa ya gaya wa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso cewa kada ya yi karfa-karfa wajen dora dan takara ba tare da an bi yadda doka ta gindaya ba amma akayi watsi da wannan shawara tasa, gwamnan ya dora wanda yake so.

“ Ina so in gaya muka ka sani, wannan magana na yi ta nanata shi. Lokacin da aka kafa APC na bada shawarar a tabbata an bi doka wajen dora shugabannin jam’iyya da zaben ‘yan takara. Amma maimakon abi wannan shawara sai aka koma aka ci gaba da yadda dama can ake yi a jam’iyyar PDP, jiya Iyau tun da dama can mun sani ba zai hafi da mai ido ba.

“ Haka akayi a lokacin zaben fidda dan takara, gwamnoni suka dora wadanda suke so, akayi watsi da yadda dokar jam’iyya tace abi ba.

” A lokacin na jawo hankalin gwamna Kwankwaso cewa ya bi doka, kada yace zai ba na kusa dashi amma ya ki ji na. Na ce masa idan ya dora na kusa dashi, ba za a sami dasawa ba.

” A wancan lokaci har Ina ba da misali da yadda ta kaya tsakanin wasu gwamnoni da suka yi irin haka amma ba a gama lafiya ba kamar Aliero da Dakingari, Ali Saadu Da Sule Lamido, Saminu Turaki Da Sule Lamido da dai sauran su. Dama mun yi wannan hasashen kuma hakan ya faru.

Hon Sumaila ya kara dacewa duk da wannan matsala da aka samu, shi yana tare da gwamman jihar Kano ne wato Abdullahi Ganduje ba Kwankwaso ba.

“ Yanzu kam Ina tare ne da Ganduje saboda yana tare da Buhari. Amma fa Buhari ne ya hada mu. Kaunar da yake wa Buhari shine yasa nima nake kaunar sa. Dama can tare ya zo ya same mu tun a lokacin da baya yin Buhari har yazo yana yin sa yanzu kaga dole muna tare kenanan.

Da yake amsa tambayar ko ficewar kwankwaso a APC zai iya yi wa jam’iyyar Illa, sai yace tabbas rasa dan siyasa a jam’iyya ya kan yi wa jam’iyya Illa tunda ita siyasa da yawanku ne kuke cin zabe, saboda haka kowa so yake ya samu karuwar mutane ba raguwa ba.

Mu Nuna Wa Matasa Illar Shan Miyagun Kwayoyi

 

Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari Dallatun Katsina ta bayyana cewar iyayen yara matasa maza da mata musamman iyayen da suka san  ‘ya’yansu na shan miyagun kwayoyi A Jihar Katsina da Nijeria baki daya da su tsawata wa ‘ya’yansu game da shan miyagun kwayoyi.

Uwargidan gwamnan jihar Katsina ta yi wannan tsokaci ne a Kwalejin makarantar ‘yan mata da ke garin Funtuwa yayin da take gudanar da jawabinta a wajen taron tsawata wa da nuna wa matasa shan miyagun kwayoyi Hajiya Hadiza ta ci gaba da cewar wajibi ne iyayen yara matasa maza da mata su sa wa ‘ya

‘yansu ido game da abokan da suke ma’amala da su domin kauce wa lalatattun abokai  wabanda ke shan miyagun kwayoyi. Sannan kuma ta umarci al’ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya da su hada karfi da karfe domin yakar ko kashe wadannan al’amura masu cutar da matasa shi dai wannan taron gwamnatin jlhar Katsina ta kirkiro shi domin samun nasarar kashe wannan al’amari na shan miyagun kwayoyi.

Taron wanda ya kunshi dukkan wani mai ruwa da tsaki a harkar tsaro na jihar Katsina kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammed Wakili da tawagarsa, jami’an hukumar kiyaye hadura jami’an tsaro na farin kaya ,hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ‘yan sintiri, da hakimai da magaddai masu hannu da shuni da sauran al’umma

Da take mai da nata jawabin a wajen taron shugabar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi Hajiya Maryam ta samu wakilcin ALH. Mustpha Maikudi  inda ya ci gaba da cewa yana rokon al’ummar jihar Katsina a duk wata kwana ko sako ko wani gurin da ba a san kome ake saida wa a gurin da su gaggauta shaida wa ofishin ‘yansanda  ko ofishin N.D.L.A Sannan ya ci gaba da cewar yana rokon gwamnatin jah ar katsina da ta taimaka ta sake masu kayan aiki na zamani kamar motoci da sauran abubuwan da za su taimaka gaya a wurin aikinsu ya tafi daidai.

Shi ma a nasa jawabin Dacta Bashir Ruwan Godiya cewa ya yi kamata ya yi a fadada irin wannan taro daga jiha zuwa kananan hukumomi  su ma su rinka irin wannan taro shi kuma shugaban kwamitin da’awa na jihar Kano Malam Aminu Daurawa cewa ya yi a kirkiro wani abu na taimako  ga duk wanda ya ce ya daina shan miyagun kwayoyi za a yi masa muhimin abu wanda hakan jihar Kano ta yi ta samu nasarar wannan al’amari. Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua Sambo Idris Sambo  ya shawarci matasa ne da su dai na irin wanan shaye-shaye domin su yi rayuwa cikin mutuncisu da samun zuri a tagari shugaban riko na karamar hukumar Funtua Abdullahi Abubukar Kutawa  ya yaba da kyayawan shirin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na kashe miyagun abubuwa irin wadannan wadanda za su taimaki kasa da al’ummar kasa baki daya sannan kuma matasan su zama ‘ya’ya nagari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: