Kociyan kulob din Arsenal ya ce ya fi jin ciwon tafiyar Kieran Gibbs akan tafiyar Chamberlain saboda a cewarsa Gibbs tun yana dan shekara goma yake kungiyar saboda haka sun shaku sosai.
Mista wenger yana wannan jawabi ne a shirye shiryen da kungiyar take na fafata wasan firimiya da kungiyar Westbrom Albion, kungiyar da Gibbs din ya koma a karshen watan agusta.
Wenger yace, duk lokacin ka shaku da abu idan zaka rabu dashi zakaji babu dadi, Gibbs tun yana dan shekara goma muke tare dashi, lokacin dayafara wasa yana buga bangaren hagu amma a gaba, sai naga kamar zai taimakamin idan na dawo dashi barin hagu a baya.
A haka na bashi horo sosai kuma ya bani gudummawa sosai, saboda haka tafiyarsa na ji haushinta sosai, amma babu yadda zanyi.
Wengan yace, ba dan wasan ne ya ce ya na son tafiya ba, sune suka ga ya kamata su bashi dama ya je inda zai dinga buga wasa duk mako domin duk dan wasan da yayi dadewar Gibbs a kungiya ya cancanta ka yi masa adalci.
Arsenal dai za ta karbi bakwancin Westbrom a yau Litinin a filin wasa na Emirates da ke birnin landan a wasan sati na shida.