Na Kashe Batun Neman Aurena Saboda ‘Son’ Madugu (Kwankwaso) – Wata Budurwa

Budurwa

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Wata Budurwa ta fito ta bayyana yadda take kaunar tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, wadda ta ce a dalilin kaunar da take masa ta ki amsar tayin aure da wani saurayi ya yi mata.

Wannan Baiwar Allah ta ce za ta iya mutuwa a dalilin son da ta ke yi wa Kwankwaso. Lubna Ali ta ce a wurinta Sanata Kwankwason ya fi karfin a ce masa Dan siyasa

Da take takaitaccen bayani a shafinta na tuwita Lubna, ta bayyana cewa a dalilin kaunar da ta ke yi wa Madugun Kwankwasiyya, ta ki amsar tayin aure da wani ya yi mata.

Wannan budurwa ta sake tabbatar da cewa ba za ta taba auren duk saurayin da bai ganin mutuncin gwarzonta ba. A cewarta, ba ta ki ta zauna babu miji a rayuwa ba, in dai sai ta auri mara ganin darajar Kwankwaso.

Lulualee kamar yadda aka san ta a Twitter ta bayyana cewa ko da ita ba ta harkar siyasa, amma tana matukar kaunar Rabiu Kwankwaso. “Na kashe batun neman aurena saboda Mai girma, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ko da bai sanni ba. Zan iya mutuwa saboda shi (Kwankwaso).” In ji Lubna Ali.

Ta ce: “Kwankwaso ya fi karfin zama dan siyasa a wurina, ina yi masa kallon jagora ne, uba, kuma abin koyi.” Wannan Baiwar Allah ta ce ta fara sha’awar tafiyar Kwankwasiyya ne tun 2003, a lokacin tana aji Daya a sakandare, ta ce a lokacin ba ta ma san kan siyasa ba.

“Amma sunan Sanata Kwankwaso ya yi ta yawo a kaina. Zan tuna motar farko da na yi, kirar 406 ce mai launin ja dauke da hoton Kwankwaso ko ina a jikinta.

Exit mobile version