Umar A Hunkuyi" />

“Na Kashe Makwabciyata Ne Saboda Ta Yi Min Zargin Satar Waya”

Fusata ne na yi ya kaini ga daba mata adda har ta mutu, wannan shi ne jawabin da wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa mai suna, Ejike Eze, ya yi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce, matashin dan asalin Jihar Ebonyi, wanda kuma yake zaune a Unguwar Ayegbami, ta Ijebu Ode, a Jihar Ogun, a gidan da yake cike da mazauna daga kabilar Igbo da Yarabawa, har na kusan shekaru hudu, yake kuma sana’ar ‘yan gwangwan. Inda a wannan safiyar ta ranar Juma’a ya jefa sauran makwabtan na shi a cikin firgici a lokacin da ya kashe daya daga cikin abokanan zaman na shi wata mata mai suna, Uwargida Adeyigba Oladipo, mai shekaru 59 da haihuwa.
Rahotanni sun nuna cewa Eze da Oladipo sun saba yin fada a tsakaninsu kusan a kowane lokaci, har zuwa wannan ranar a lokacin da matar ta zargi Eze da sace mata wayarta.
Wannan zargin ne ya fusata Eze, inda aka yi zargin ya kai mata harin da ya yi sanadiyyar mutuwarta. A bayan ya kashe ta din ne rahotanni suka nuna cewa sai ya ranta a na kare daga wajen. Amma a bayan kwanaki biyu sai ‘yan sanda suka kama shi a tashar motar Ijebu Ode, yana shirin barin garin domin komawa inda ya fito.
Matashin ya zargi kusan dukkanin makwabtan na shi da ‘ya’yansu da cewa duk makiyansa ne, yana mai cewa ya ji zafin bai sami kashe su baki-dayansu ba.
A cewar sa, “An kawo ni nan ne sabili da na kashe makwabciyata, ta hanyar daba mata adda. Ta kasance takan zarge ni ne da satan mata kayayyakin ta, a duk lokacin kuma da ta yi mani irin wannan zargin sai sauran makwabtanmu da muke zaune a cikin gida guda su goya mata baya. su yi ta zagina suna yi mani ihu.
Da yake labarta yanda lamarin ya auku, Eze ya ce, “A wannan ranar, sai matar ta zarge ni da satar mata waya, sai na fusata. Daganan sai na dauki adda na kai mata farmaki inda na sare ta a kai. Abin ya auku ne da misalin karfe 5 na safiya, sai tana ta ihun neman taimako. daya daga cikin makwabtan namu ya fito domin ya taimaka mata, shi ma sai na yi kansa da adda har ya gudu.
“Idan da zan sami damar ganin sauran makwabtan nawa duk sai na kashe su da adda. Har ma na sake kai wa dayansu da ya nemi ya yi fada da ni farmaki a bayan da na kashe ta din, amma sai ya gudu, na ji zafin samun arcewar na shi, idan da na tarar da shi da na kashe shi.
Da ake yi masa tambayoyi, Eze ya amsa aikata kisan matar da adda domin wai ta yi masa zargin satar waya. Ya ma kara da amsa cewa shi ne ya datse hannayen matar duka biyu wai domin ta yi kokarin kwace addan daga hannunsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Oyeyemi, ya ce ‘yan sanda sun shiga cikin maganar, don haka ba su damu ba ko da iyalan mamaciyar ba sa son yin shari’ar da shi, ko kuma suna so.

Exit mobile version