Daga Mustapha Ibrahim Kano
In dai za’a iya tunawa a kwanankin baya ne Ministan aikin gona na Najeriya Chief Abdu Ogbe ya bayyana cewa akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya, ta hana shigowa da shinkafa kwatakwata cikin kasar nan, a wani kokari na Gwamnatin tarayya na ta ga an bunkasa noman shinkafa da kuma dogaro da shinkafar da ake nomawa a kasar nan, akan haka shugaban kungiyar manoma na kasa reshen Jahar kano AFAN kuma shugaban kungiyar masu noman Alkama shi ma ya bayyana ra’ayinsa. Irin makudan kudade da ake kashewa wajen shigo da shinkafa da alkama sun kai kimanin naira biliyan Takwas a duk shekara, haka ita ma alkama don haka muna goyan baya, kuma muna maraba da hana shigo da shinkafa a kasar nan.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jahar kano wato All Farmer Association of Nigeria (AFAN) ALhaji Faruku Rabiu Mudi, lokacin wata ganawarsa da manema labarai a ofishin kungiyar da ke birnin kano. Shugaban AFAN ya ce shigo da Shinkafa da Alkama akwai siyasa domin duk abinda ake shigo da shi to ana karya farashin sa ne, yadda idan ka e za ka sayo za ka samu an karya shi, kuma wanda aka shigo kasar, ya kara tsada fiye da kai naka domin ta haka ne, za a karya naka na gida, kuma ku kasance kuna dogaro da na kasashen waje, kuma hakan akwai matsala, shi ya sa mu muna goyan bayan ,a hana shigo da Sshinkafa domin hakan zai sa ta mu ta gida ta yi daraja, kuma a samu yawan manoma da kayan noma, yadda zamu dogara da kanmu, domin duk kasar da bata dogara da kanta, ta fuskar abinci to da akawai babbar matsala a gare ta.
Don haka ne ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin daka na sai mun dogara da kan mu ta fuskar abinci, ya ce duk da ba muna goyan bayan mutane, su sha wahala bane amma dai muna goyan bayan a samu wadata da dogaro, da kai ta fuskar noma, ya ce domin manomi shi ne ya fi kowa tasiri da kyakkyawar rayuwa, saboda idan ka samu manomi a gona yana aikin dibar tumartir ko dibar gyada ,ko kuma shinkafa, da dai sauransu, to manomi zai iya diba ya baka, amma dan kasuwa, a kasuwa na yadi ko na Atamfa ko makamancin haka, idan ka same shi a kasuwa to ba zai baka ba, don haka ba mu goyan bayan masu karamin karfi su cigaba da dandana kudarsu .