A Na Kashe Naira Biliyan Takwas  Wajen Shigo Da Shinkafa

Daga Mustapha Ibrahim Kano

In dai za’a iya tunawa a kwanankin baya ne Ministan aikin gona na  Najeriya Chief Abdu Ogbe ya bayyana cewa akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya, ta hana shigowa da shinkafa kwatakwata cikin kasar nan, a wani kokari na Gwamnatin tarayya na ta ga an bunkasa noman shinkafa da kuma dogaro da shinkafar da ake nomawa a kasar nan, akan haka shugaban kungiyar manoma na kasa reshen Jahar kano AFAN kuma shugaban kungiyar masu noman Alkama shi ma ya bayyana ra’ayinsa. Irin makudan kudade da ake kashewa wajen shigo da shinkafa da alkama sun kai kimanin naira biliyan Takwas a duk shekara, haka ita ma alkama don haka muna goyan baya, kuma muna maraba da hana shigo da shinkafa a kasar nan.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jahar kano wato All Farmer Association of Nigeria (AFAN) ALhaji Faruku Rabiu Mudi,  lokacin wata ganawarsa da  manema labarai a ofishin kungiyar da ke birnin kano. Shugaban AFAN ya ce shigo da Shinkafa da Alkama akwai siyasa domin duk abinda ake shigo da shi to ana karya farashin sa ne, yadda idan ka e za ka sayo za ka samu an  karya shi, kuma wanda aka shigo   kasar, ya kara tsada fiye da kai naka domin ta haka ne, za a karya naka na gida, kuma ku  kasance kuna dogaro da na kasashen waje, kuma hakan akwai matsala,   shi ya sa mu muna goyan bayan ,a hana shigo da Sshinkafa domin hakan zai sa ta mu ta gida ta yi daraja, kuma a samu yawan manoma da kayan noma, yadda zamu dogara da kanmu, domin duk kasar da bata dogara da kanta, ta fuskar abinci to  da akawai babbar matsala a gare ta.

Don haka ne ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin daka na sai mun dogara da kan mu ta fuskar abinci, ya ce duk da ba muna goyan bayan mutane, su sha wahala bane amma dai muna goyan bayan a samu wadata da dogaro, da kai ta fuskar noma,  ya ce domin manomi shi ne ya fi kowa tasiri da kyakkyawar rayuwa, saboda idan ka samu manomi  a gona yana aikin dibar tumartir ko dibar gyada ,ko kuma shinkafa, da dai sauransu, to manomi zai iya diba ya baka, amma dan kasuwa, a kasuwa na yadi ko na Atamfa ko makamancin haka, idan ka same shi a kasuwa to ba zai baka ba,  don haka ba mu goyan bayan masu karamin karfi su cigaba da dandana kudarsu .

Ya ce idan Jama’a su ka daure farashin abinci zai sauko domin ana kara noman ne, abinci na kara yawa kuma farashin na raguwa,  don haka yanzu burinmu a kawo hanyar saukaka kashe kudi a noma, da kuma bunkasar samun amfanin gona fiye da yadda ake samu, a baya ta hanyar dabarun  noma na zamani. Ya cigaba da jaddada kuma  cewar, wani abin takaici shi ne barin kano a baya, wajen samun rancen noma na Gwamnatin tarayya inda Anambra ta samu rancen Naira Biliyan Tara zuwa 11 Kebbi Naira Biliyan 14, wannan  abin ya faru ne, sakamakon ana basu bashin suna biya, mu kuma nan kano mun karbi bashin kasa da Biliyan daya, kuma an kasa biya duk da yanzu an dauki matakan ba sani ba sabo, na duk wanda ya ci  bashi, sai ya biya domin wannan bashi na Anchobrower ko wacce Jaha tana samun karuwar sa ne, ta hanyar in ta biya a kara mata, har ta kai wani matsayi, to kano ta zama koma baya ta wannan harka, don haka akwai bukatar daukar matakai don cigaba. Haka kuma ya ce yanzu haka kungiyar AFAN da hadin guiwar jami’an tsaro na daukar matakan kame masu hada takin zamani na jabu a kano.

Exit mobile version