Abba Ibrahim Wada" />

Na Koma Juventus Domin Lashe Kofin Zakarun Turai Ne – Kulusebski

Sabon dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Dejan Kulusebski, ya bayyana cewa ya koma kungiyar ne domin lashe kofin zakarun turai na Champions League da kuma ragowar kofunan kasar Italiya.

Kungiyar Juventus ta sayi dan wasan tsakiyar dan kasar Sweden Dejan Kulusebski daga kungiyar kwallon kafa ta Atalanta a kan yarjejeniyar yuro miliyan 35 sakamakon kokarin da yayi a wannan kakar.

Dan kwallon mai shekara 19 a duniya ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi da kungiyar Serie A, amma zai koma kungiyar kwallon kafa ta Parma a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa.

Kulusebski ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara daya da Parma a watan Yulin shekara ta 2019 kuma ya zura kwallaye 17 sannan ya fara buga wa Sweden wasa ne a watan Nuwamba a wasan neman shiga gasar Euro 2020.

“Juventus babbar kungiya ce a duniya wadda kowanne dan wasa yake fatan bugawa wasa saboda tarihinta da sunanta da kuma irin ‘yan wasan da suke cikinta saboda ina fatan lashe kofin zakarun turai a kakar wasa mai zuwa idan na fara buga wasa” in ji Kulusebski

Kudin da za a biya Kulusebski zai iya kai wa yuro miliyan 44m (fam miliyan 37), amma hakan ya danganta da yadda dan kwallon ya cika wasu sharudda na kokari ta hanyar zura kwallaye a raga da kuma taimakawa kungiyar lashe kofuna.

Exit mobile version