Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Shahararren kansilan nan na Jihar Kano, wanda ke wakiltar Mazabar Guringawa dake Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Muslihu Yusuf Ali, ya bayyana cewa, ya nada mataimaka har guda 18 ne, don kusanto da alummarsa na yankin ne ga gwamnati, wanda hakan zai ba su damar cin moroyarta. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kansilan a tattaunawarsa da LEADESHIP A YAU jiya a birnin Kano.
Haka zalika, an bayyana cewa, mazabar Guringawar a matsayin mazabar da ta fi dukkanin mazabun Jihar Kano guda 484 dacen wakili. Jawabin hakan ya fito daga bakin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Shamsu Abdullahi Sa’ad, a lokacin bikin kaddamar da mataimaka da mashawarta 18 din da za su taimaka wa kansilan mazabar gudanar da kyakkyawan Jagoranci.
“Ina alfahari da kasancewa ta dan wannan mazaba, wadda ke zaman fitilar dake haske cigaban Karamar Hukumar Kumbotso. Ganin wadannan zakakurai da aka zakulo ya nuna Guringawa ta zama allurar dinke duk wata baraka a Karamar Hukumar Kumbotso,” inji shi.
Don haka sai ya bukaci wadanda aka zabo da su yi duk mai yiwuwa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Shi ma, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin taron, Hon. Muslihu Ali, wanda kuma shi ne Bulaliyar Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar, ya ce, kokarin da yake na tabbatar da ganin an kusanto da jama’a kusa da wakilansu ya sa a waccan rana ta Alhamis ya kaddamar da mutane 18, wadanda aka zakulo daga lungu da sakon mazabar Guringawa tare da damka masu takardar kama aiki a matakai daban-daban.
Alhaji Muslihu ya bayyana cewa, “wannan lokaci ne na samar da sabuwar Kumbotso a karkashin jagorancin gogaggen dan kishin kasa da al’ummar Kumbotso, Hon. Garban Kauye Farawa, hakan ta sa na ga da cewar, samar da mataimaka da za su lura tare da ba mu shawarwari, domin al’ummarmu su amfana da romon dimukradiyya.”
Ya cigaba da cewa, an zakulo wadannan mutane 18 bisa cancanta da kuma kyakkyawan zaton da ake yi masu na bayar da gudunmawar da ake bukata. Saboda haka sai ya bukace su da su tabbatar da ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Haka kuma ya bukace da su zama wakilai na gari kasancewar za su wakilci al’umma ne ba kawunansu ba.
Wadanda aka kaddamar din a lokacin bikin sun hada da Sulaiman Ibrahim Bako, Yahaya Abdu Yahaya, Kamalu Garba LY, Usman Umar Zubairu, Dalhatu Yakubu, Bashir Ali, Ameee Sani Ahmed, Hon Garba Danmarke, Stephen Mayowa Olawale, Bashir Usman Guringawa, Mariya Uba, Nasir Abubakar, Alhaji Magaji Uba, Sunusi Ado, Hon. Adamu Abubakar, Saifuddeen Sani Gunduwa da Aliyu Saleh.
Cikin wadanda suka gabatar jawabai a wurin taro akwai shugaban Jam’iyyar APC, Shugabar Mata da sauran jiga-jigan jam’iyyar a mazabar ta Guringawa.