Bala Kukuru" />

Na Rike Sana’ata Ta Sayar Da Kankana

Shugaban masu sayar da kankana Oga Hassan da ke garejin motocin tifofin daukar yashi bayan asibitin dabbobi dake garin Funtuwa a jihar Katsina ya ce kankana wata aba ce mai muhimmanci a jikin dan’adam wajen kara jini da ruwa a jiki da sauran abubuwa a jikin dan’adam sannan kuma ana iya safarta bawonta yakoma wasu magun guna dake kare wasu kananan cututtuka dake jikin dan adam acewa Oga Hassan hakan yasanya yarike wannan sana’ar ta sayar da kankana.

Ya ci gaba dacewa a bangarenshi yasamu kudin da zai ci gaba da tafiyar da harkokin rayuwarsa data iyalinsa saboda haka yake kira ga yan kungiyarsa aduk inda suke surike wannan sana’ar ta sayar da kankana hannu bibiyu saboda akwai rufin asiri a cikinta a cewasa hakan ya sanya suka samu ci gaba sosai a cikin wannan sana’ar sannan yacigaba da gode wa Allah subhanahu wata’ala bisa ga wannan bai wa da suka samu wajan Ubangiji.

A Hassan ya kara dacewa ta bangaren siyasa kungiyarsu ta masu sayarda kankana suna bada gudunmowa sosai musamman a lokacin zabe kuma su yan’asalin jam’iyar A.P.C ne tunda suke basu taba sauya sheka ba sukoma wata jam’iya amma haryanzu acewarsa basu taba samun wani tallafi daga gwamnatin jahar katsina ba yacigaba da bayanin cewa gashi kuma gwamnatin nata bawasu yan kasuwa bashi.

Ya kara da cewar hakan yasanya yacebari ya mika kokon bararsu ga wannan gwamnatin ta jihar Katsina mai tausayin talakawa da sauran al’umma cewar suma suna bukatar irin wannan tallafin da gwamnatin jahar katsina ke badawa domin suma su kwankwadi romon dimukuradiyar jihar Katsina

Sannan ya ci gaba da kira ga yan kasuwa da sauran al’umma da su ci gaba da ba wadannan gwamnatocin hadin kaida goyon baya domin su cim ma burinsu na ciyar da kasar nan gaba acewarsa suma yankasuwa suna da hakki na taka rawa maikyau wajan tallafawa gwamnati ta kowanne bangare Allah ya taimaki karamar hukumar funtuwa da jahar katsina da najeriya baki daya

 

Exit mobile version