Yusuf Shuaibu" />

‘Na Saci Mashin Ne Don Biyan Kudin Haya’

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nija ta samu nasarar cafke wani mutum bisa zargin sa da sace babur kusa da babbab asibitin Suleja cikin karamar hukumar Suleja dake Jihar Neja. Shi dai wanda ake zargi sunan sa Celestine Eze dan shekara 32, wanda ya sace wa Ibrahim Gajere Fadama Suleja babur din sa kirar Bajaj. An labarta cewa shi dai wanda ake zargi yana tsaya ne a filin asibiti kafin jami’an ‘yan sanda su kama shi.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa a ranar Talata ne wanda ake zargin ya shiga cikin asibitin tare da nuna cewa shi majinyaci ne. Bincike ya nuna cewa shi dai wanda ake zargi ya fito ne daga Abuja kusa da filin jirgin sama sai ya zo Suleja ya aikata wannan laifin. Wanda ake zargin ya bayyana wa manema labarai cewa dalilin da ya sa ya saci wannan babur shi ne domin in biya kudin hayan gidana.
“Abubuwa sun cakude min, har takai ga ban iya biyan kudin hayan gidana, gashi kuma babu aiki kota ina, ga matsaloli sun yi min yawa saboda haka na yanke shawara da in yi sata, gaskiya abu bane mai kyau,” inji shi.
Shi dai wanda ake zargi ya fito ne daga kuda maso gabas na kasar nan inda ya ce “tun lokacin da na zo cikin garin Abuja nake ta fadi tashi domin in samu aikin da zai rufawa kai na asiri amma kuma aikin bai samu ba, sai ma al’amura suka kara jagulewa, sai fara tunanin kamar na yi babban zunubi a kan kaddarata, in ba barawo bane amma yanayin yadda na tsinci kaina shi ya sani sata.”
Kakakin rundunar ‘yan sanda Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, in ya kara da cewa in samu nasarar amso babaur din daga wajen wanda ake zargi. Abubakar ya ci gaba da cewa idan sun sama binciken lamarin za su muka shi zuwa kotu.

Exit mobile version