Na Samu Nasarori Masu Yawa A Jagorancin kungiyar ’Yan Gwangwan – Bala Abubakar

Shugaban kungiyar masu gudanar da harkokin kasuwancin gwangwan na unguwar Abarmasoya Alasaya Aja ta karamar Hukumar Itiwosa dake cikin garin Legas Bala Abubakar, ya bayyana cewa a halin yanzu yana cigaba da samun nasarori mai yawa a jagorancin kungiyar a Legas da kewayanta baki daya.

Bala Abubakar, ya yi wannan ta’aliki ne a ofishinsa dake Unguwar Aja jim kadan bayan kammala taronsu da mambobin kungiyar da suka saba yi a duk bayan mako biyu da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata.
Shugaban ya ce cigaban da yake ganin ya fara samu shi ne kafin samun jagoranci a kungiyar tana fama da ‘yan rikice-rikice nan da can, ya ce a halin da ake ciki yanzu babu wata rigima, yana mai cewa, sannan kuma a lokacin jagorancinsa ne mambobin kungiyar suka samu jituwa a tsakaninsu, bugu da kari, a lokacin jagorancinsa ne mambobin kungiyar suka samu sauki wajen samun yawan kame-kamen da ma’aikata suke yi masu.
Ya kara da cewa, Alhamdulillahi a jagorancinsa an samu zaman lafiya a tsakanin al’ummar Hausawa da sauran kabilun mazauna unguwar Aja da kewayanta, da fatan Allah ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya gaba daya.
Kazalika ya nuna rashin shin jin dadi a game da abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’ummar Hausawa da sauran kabilun mazauna jihohin Kudu da Yammacin Nijeriya, ya ce musamman a baya-bayan nan wanda ya faru a jihohin kasar Inyamurai a lokacin zanga-zangar ENDSARS da kuma wanda ya faru a garin Ibadan a Unguwsr Shasha, al amarin da ya sanya Yarabawan yankin a bisa kan abin da bai taka kara ya karya ba su kai ta kisan ‘yan Arewa mazauna yankin na Shasha tare da kone masu dukiyoyi su kuma ‘yan uwan su suna can Arewa suna shan shagalin su babu wata tsangwama da fatan Allah ya saka wa ‘yan Arewa da alheri abisa dukiyoyin da aka yi masu asara. Sannan shugaban kungiyar ya shawarci mambobin kungiyar tare da sauran al’ummar Hausawa mazauna Legas da su cigaba da hada kawunan junansu wajen gudanar da harkokin su na yau da kullum domin kauce wa irin wannan wulakancin da kabilun kasar nan suke yi musu, da fatan Allah ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya.

Exit mobile version