Abba Ibrahim Wada" />

Na San Kungiyar Da Zan Buga Wa Wasa A Kakar Wasa Mai Zuwa – Griezman

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Antonio Griezman ya bayyana cewa yasan kungiyar da zai koma domin ya bugawa wasa a kakar wasa mai zuwa bayan ya tabbatar da cewa bazai zauna a Atletico Madrid ba.

A karshen kakar data gabata ne dai dan wasa Griezman, ya bayyana cewa bazai iya cigaba da zama a kungiyar ba saboda yanason ya koma wata kungiyar domin ya cigaba da buga wasa kuma tun farko Barcelona ce take zawarcinsa.

Dan wasan mai shekara 28 a duniya ya shafe shekara biyar a Atletico Madrid inda ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar Laliga da gasar cin kofin Europa sanann kuma sukaje wasan karshen na kofin zakarun turai sau biyu.

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Enrikue Cerezo ya tabbatar da cewa har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bata tuntubesu ba akan dan wasan sai dai dan wasan da kansa ya bayyana cewa yasan kungiyar da zai koma.

“Nasan kungiyar da zan bugawa wasa a kakar wasa mai zuwa saboda haka ba sauri nake ba kuma komai ina binsa a hankali kawai dai abinda nasani shine bazan kasance a Atletico ba a kakar wasa mai zuwa” in ji Griezman

Ya cigaba da cewa  Atletico Madrid tayi masa komai a rayuwarsa saboda haka bazai taba mantawa da kungiyar ba da kuma abinda tayi masa na mayar dashi babban dan wasa wanda duniya ta sanshi.

Farashin dan wasan dai yanzu ya kama fam miliyan 106 kuma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tayi alkawarin zata biya kudin idan har ya amince zai koma kasar Faransa da buga wasa sai dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester United har yanzu bata hakura da neman dan wasan ba wanda ya lashe kofin duniya a shekarar data gabata da tawagar kasar Faransa a Rasha.

Exit mobile version