Na Sha Guba Sanda Na San Matata Ta Mutu – Wanda Ake Zargi

Kayayyakin Da Aka Wawure

Daga Rabiu Ali Indabawa

Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Bayelsa ta cafke wani mutum, Christopher Chiabata, bisa zargin kashe matar sa mai shekaru 41 da wata Kwari. Chiabata, mai shekaru 59, yana daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifi da Kwamishinan ‘yan sanda, Mike Okoli ya gabatar a hedkwatar rundunar da ke Yenagoa ranar Laraba.

Ya ce ya kashe matar tasa ne don kare kanta yayin fada kan kudi a gidansu da ke Onuebum a Karamar Hukumar Ogbia da ke jihar. A cewar rahoton ‘yan sanda, Chiabata ya bugawa matar tasa makamin a yayin da suke fadan, kuma bayan sun fahimci cewa ya yi kisan kai, sai ya sha Sniper don kashe kansa amma makwabta suka tashi tsaye suka mika shi ga ‘yan sanda.

Ya bayyana a wata hira da ya yi da cewa ya yi aure da matarsa ​​tsawon shekara 30 tare da ’ya’ya biyar amma suna yawan fada saboda tana da dabi’ar hana shi samun kudaden da suka hada hannu daga sana’ar su ta noma.

Chiabata ya ce, “Duk lokacin da matata ta kai kayanmu kasuwa, ba ta ba ni labarin tallace-tallace yadda ta sayar da kuma yadda adadin kudaden suke. Tsaho shekara biyu da muka yi cikin aiwatar da wannan kasuwanci ta ki ba ni lissafin kudin da muka samu daga gonar. Don haka, wata rana, na kira ta don ta ba ni lissafi nan ma sai ta ki, daga nan ne sai muka fara fada har sai da makwabta suka raba mu.

“A cikin fushi, washegari, na roke ta da ta bar harkar gonar domin ni kadai na ci gaba da rikewa. Wata rana, lokacin da na dawo daga gona, sai ta tattara kayana a waje. A wannan ranar, mun sake yin fada kuma makwabta sun rabu sun daidaita mu.

“Na gaji da duk abin da yake faruwawa tsakanimu, na ce mata ta fita daga gidan washegari amma ta ki. Daga nan muka fara fada a wancan lokacin. Ta fi karfina; don haka, duk lokacin da muka yi fada, za ta doke ni ba tare da tausayi ba. Wannan karon, yayin da take dukana, saboda fusata, sai na buge ta da makami.

“A lokacin ne ta fadi. Makwabta sun taimaka aka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal inda ta mutu. Lokacin da na ji ta mutu, sai na dauki maganin kwari ina kokarin kashe kaina amma makwabta suka yi saurin kawo min dauki suka dauke ni zuwa asibiti.”

Okoli ya kuma gabatar da wani mai suna Lazarus Josiah, mai shekaru 29, wanda aka kama bisa zargin ya shake mahaifiyarsa mai shekaru 59, Chain Bishop, har lahira saboda wasu dalilai da har yanzu ba a gano su ba a yankin Odioma da ke Karamar Hukumar Brass ta jihar.

Haka kuma an cafke wasu mambobin kungiyar gungun mutane 5 wadanda suka kware a harkar yin sojan gona a matsayin jami’an Hukumar Kula da Tsabtar Muhalli ta Jihar don sacewa tare da yin fashi a kan masu amfani da hanya a kusa da Yenagoa, babban birnin jihar.

Exit mobile version