Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna – Inji Aisha Galadima

Daga Amina Bello Hamza

Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna–Inji Aisha Galadima
Aisha Galadima na daya daga cikin wanda mata ke kira ya zuwa takara a majalisar jihar kaduna don kwato masu yanci hakan yasa wakilinmu Idris Umar Zariya ya zanta da ita a makon da ya gabatar akan ko me yasata shiga harkar siyasa a matsayinta ta mace? Ga yadda hirar tasu ta kasance.
Hajiya ko zaki gayawa masu karatu sunanki da tarihinki?

Hajiya Aisha Galadima

To da farko dai sunana A’isha Umar Galadima, kuma an haifeni a Tudun Wada cikin jihar Kaduna. Na yi makarantar Primary na yi kuma Secondary, sannan kuma na je jami’ar Ahmadu Bello Zariya na karanta Political Science, an haifeni a shekarar 1988, 22 ga watan biyu.
To Hajiya ga yadda jama’a suke bibiyarki a kafar sada zumunta ya nuna cewa ke mace ce mai sha’awar yin siyasa, me ya sa kike sha’awar yin siyasa Hajiya?
E a gaskiya ni mace ce mai sha’awar yin siyasa kuma ni ‘yar kasuwa ce. Abinda ya sa nake sha’awar yin siyasa ina so in kara fadada ayyukana na alkhairi wanda ya kasance baka iya yin su sai kana cumin gwamnati. So na kasance ina yin sana’a har na kan yi kokari na kafa wani foundation dina ana kiransa A’isha Galadima Foundation, wanda na kan yi kokari in taimaki marayu da marasa karfi, so wannan dalilin ya sa na ce bari in shiga siyasa domin in kara fadada ayyukana na alkhairi da na ke yi. To kuma zan ce na fara siyasa shekaru 15 da suka wuce bani da shekaru da yawa, na fara na shiga jam’iyyar Buhari ANPP, muka dawo CPC muka dawo APC, to a wannan lokacin alal hakika idan Buhari ya fito takara na kan zama nice shugabar mata a jihar Kaduna. Kamar shekara ta 2011 da shekara ta 2015, bayan an kafa gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai gwamnatin ta jihar Kaduna ta nada ni a matsayin board member Kaduna Water Corporation, to a takaice kenan.
To Hajiya a yanzu haka kina takarar neman wata kujera ne a jihar Kaduna?
Eh to zan ce e ne zan ce a’a saboda mutane ne al’umma saboda yadda suka ga ina da jajircewa saboda mutane su samu saying rayuwa saboda yadda in ka duba ka gani da yawanmu mata mune muke shan wahala, ganin haka sai mutane suka ruka taruwa suke cewa in fito takara tun shekara 6 da ta wuce 2015, saboda in wakilcesu, to kuma gaskiya hankalina bai waiwaya ba to a wannan karon sai linguistic suke ta nuna sha’awar in fito takara in wakilcesu, to amma gaskiya har yanzu ban yanke shawara zan fito ko ba zan fito ba, wanda hakan ya sa na ga wasu na ta yin poster suna bada gudummuwa suna so na wakilcesu a wannan yanki da nake, so ka ji dalili.
To wane matsayi suke so ki wakilcesu shugabar karamar hukuma ko ‘yar majalisa?
Yar majalisar jiha suke so in fara wakiltarsu tukunna wanda haka na gani sun fara yin poster suna turowana ce to! Nima gaskiya da na fara gani abin ya bani mamaki, suka fara turomin ta WhatsApp dina, to tun dai ina cewa a’a, suka ce su fa suna son sai na fito wannan takara.
So Hajiya da yawa mutane suna ganin karatun ‘ya mace ko kuma siyasar ‘ya mace yana dankwafe darajar ‘ya mace me za ki ce game da irin wannan tunani, ma’ana mace ta fito fagen siyasa yana rage mata kwarjini da sauransu ko kuma a ce karatun ‘ya mace?
Eh to, ka ga ita mace za a ce misali tana da wai rauni ko? To kuma ka ga kasar mu Nijeriya muna tafiya ne tare da addininmu da al’adunmu, kuma ko bayan siyasa ita mace tana da wani mutunci da Allah Ya ba ta na daban, to idan ta yi kokari ta kare mutuncinta da darajarta za ta samu, kuma ni siyasa bata rage min kwarjini na ba saboda ina yin abubuwa na da natsuwa kuma ka gan ni na yi karatun addini har na yi saukar Alkur’ani har na yi hadda, na yi hadda na Susan izu 40, sai wasu abubuwa suka dan dakatar da ni. Ka ga duk mutumin da Allah Ya sa kana da tsoron Allah a al’amurran ka babu wasu abubuwa da za a ce ka yi shi wanda zai zame maka matsala. Duk wani abin da za ka yi in kasa natsuwa, da tunani da adalci da gaskiya babu wani abu, kuma wajibi ne, idan mata ba su yi karatu ba ai al’umma ta zama sai a hankali, sai mace ta yi karatu za ta san ya za ta yi ko ‘ya ‘yan ta ta tafiyar da su da tarbiyya. So ni ban ga wata matsala ga karatun ‘ya mace da tarbiyyarta ba gaskiya saboda in ka duba ka gani mu da yawa kuma in duba ka gani da yawan matan da suka ce in fito sun ce su suna zaben mazajen amma sai su kasa ganin su ma, idan suka yi complain ko in sun kira su a waya basu dauka sai su ce su saboda suna da mata kuma a ce mata su kira su a waya matsala ne. Ka san halin mata da maza a gida. To shine matan suka ce bari su zabi mace wadda sun san jajirtacciya ce kuma basuda wani shamaki wadda indai Allah Ya bata wannan kujerar za ta iya yi musu adalci, so ka ji dalili kenan.
To Hajiya menene ya burge ki ki ka tsaya tsayin daka wajen wayarwa da mata kai wanda har ya sa suke son ki wakilce su a wata matsaya?
Eh to gaskiya ko idan ka kalli mata za ka ga ‘ya ‘yanmu ne, mu bama daukar makami idan ana rigima mu ake kashewa ‘ya ‘ya da sauransu. Kuma mace inda ba wadda ta zama wata iri ba za ka same ta tana da tausayi da jin kai, haka ne? Kuma gaskiya abinda ya kara burgeni gaskiya ina so in ga na bada gudummuwa na yara matasa… bana so in ga yara matasa suna zaune zaman banza ba karatu ba wasu abubuwa, to abubuwan da suke burgeni ina son in ga cewa Allah Ya bani wata dama wadda zan ga na yi hobbasa yadda zan ga na rage ma wasu zaman banza duk da yanzu ina iyakar kokarina in ga cewa damar da na samu in inganta rayuwar wasu, rayuwarsu ta zama ingantacciya musamman wajen ilimin nan za ka ga wasu yaran marayu ne iyayensu da suka mutu basu iya biyan kudin makaranta, to wannan duk yana daga ciki. To kuma ina son in ga na tallafawa mata da wasu kananan jaruka na sana’o’i idan Allah Ya bani dama yadda za su tallafawa rayuwarsu su dogara da kansu. So akwai abubuwa da yawa wanda nake so in gani nima a kashin kaina wanda in ka duba ka gani misali gwamnatin jihar Kaduna ai akwai mata a ciki amma in ka duba ka gani matan da ake dakkowa ba mata ba ne wadanda za su runka jin koke koken al’umma, haka ne? So idan aka dakko masu zuciya da kishi aka basu wata dama za su yi kokari su kwatanta saboda gaskiya mu munada tausayi fiye da maza. To kuma ni gaskiya kullum burina in ga yaranmu da matasanmu suna zuwa makaranta basu zaman banza a rage radadin nan. Kuma wallahi ina bakin cikin in ga yaran mu sun zama ‘yan shaye-shaye, basu karatu basu dogaro da kai sun zama sai a hankali so wannan abin yana daga min hankali idan na ga yaranmu cikin wannan halin.
Zamu cigaba a mako mai zuwa

Exit mobile version