Connect with us

LABARAI

Na Shirya Tsaf Don Kwace Kujerar Dogara, Inji Barista Gashion

Published

on

Wani matashin Lauya, Barista Gashion Daniel Danna ya nuna sha’awarsa ta tsaya neman kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dass, Tafawa Balewa da kuma Bogoro a babban zaben 2019 da tafe, a karkashin lemar PDP.
Ita dai wannan kujerar da matashin ke nema, ita ce kujerar da Kakakin Majalisar tarayya, Barista Yakubu Dogara ke wakilta, inda matashin ya nuna kwarin guiwarsa ta samun gagarumar nasara a babban zaben da ke zuwa.
Matashin dan shekara 37 mai suna Barista Danna ya nuna sha’awar tasa ne a jiya a lokacin da ke dawo da fom din tsayawa takarar wa uwar jam’iyyar PDP a sakatariyarsu da ke Bauchi, ya ce “Na yanke shawarar fito neman wannan kujerar ne a sakamakon dumbin magoya baya da daga mazabata da suke ta kiran na fito na nemi wannan kujerar sama da shekaru biyu, duk lokacin da na ziyarci yankin sai sun nemi na fito domin na wakilcesu, suna neman na tsaya ne a bisa imanin da suka yi na zan kyautata shuganci da kuma tabbatar da wakilci na gari,” Inji Barista
Dan takarar ya nuna kwarin guiwarsa ta samun nasarar wannan kujerar da Dogara yake a kai yau muddin ya samu goyon bayan jam’iyyar tun daga wakilai, masu zabe da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Ya ce lokaci ya yi da za su amshi kujerar daga hanun Dogara domin ci gaba da gina yankin na Tafawa Balewa, Dass da Bogoro, yana mai kuma shaida cewar za su yi gagarumar bayar da gudunmawa wajen kyautata shugabanci da zarar aka basu wannan zarafin.
Gashion Danna ya ce baya fito neman wannan kujerar ne ‘ko-a-yi-rai’ ‘ko-a-mutu-ba ne’, illa dai ya biye wa ra’ayin jama’an da suka yi ta bukatarsa na ya fito domin kyautata shugabanci, ya kuma tabbatar musu da cewar zai yi amfani da kwarewarsa wajen ganin nasararsu ta samu kaiwa ga gaci.
Da yake tasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Akoshe Akuyam wanda mataimakinsa Alhaji Haruna Musa Shitu ya wakilta, ya nuna gayar farin cikinsu a bisa nuna sha’awar matashin na neman tsayawa a karkashin jamiyyar ta PDP, yana mai bayanin cewar PDP za ta bayar da dama wajen zaban dukkanin wanda jama’a suke so a zaben fidda gwani, ya ce ba za su yi kama daura ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: