Khalid Idris Doya" />

Na Warke Daga Cutar Coronavirus, In ji Gwamnan Bauchi

Labarin da ke fitowa daga jihar Bauchi na cewa gwamnan jihar Bala Muhammad ya warke daga cutar Coronavirus.

Gwamna Bala da kansa ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter da karfe 6:14 pm din yau din nan.

Ya ce “Alhamdullah. Na karbi sakon gwajin COVID-19 karo na biyu inda sakamakon ya tabbatar na Warke daga cutar. Ina godiya gareku a bisa addu’o’i da goyon baya da kuka nuna min a lokacin da ke killace.

“Abu mai gayar muhimminci shine godiya ga Allah madaukaki a bisa ni’imarsa gareni,” A cewar Gwamnan.

Kawo yanzu dai Gwamna Bala ya sanar da warkewarsa.

Exit mobile version