Umar Mohammed Gombe">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home AL'ADU

Na Yaba Da Nagartar Wannan Kungiya Ta RAYAAS – Matar Gwamnan Bauchi

by Umar Mohammed Gombe
January 5, 2020
in AL'ADU
4 min read
Na Yaba Da Nagartar Wannan Kungiya Ta RAYAAS – Matar Gwamnan Bauchi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Dakta Aisha Bala Mohammed ta yaba da nagartar Kungiyar Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association (RAYAAS) bisa ayyukan alheri da suke yi don rage wa gwamnatoci dawainiya, yana mai cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya aiwatar da komai ba, har sai an samu ire-iren wannan kungiya don yin abubuwan da suka kamata ga al’umma.

Uwargidan Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin Babban taron kungiyar na Kasa karo na biyu, da ya gudana a dakin taro na Otel din Zaranda dake garin Bauchi a ranar Asabar na makon jiya.

samndaads

“Ban yarda na amsa wannan gayyata da ku ka yi mani ba, sai da na bincika na tabbatar da cewa ba kungiyar banza ba ce, sannan na zo. Kuma ina kara yaba maku bisa kokarin da ku ke yi na hadin kai da taimakon juna, koyar da tarbiyya da kuma rungumar sana’o’i don kauda marasa daga shaye-shaye da zaman banza.” In ji ta.

“Kuma wadannan ayyuka ne muka sanya a gaba tun da mai gidana ya zama Gwamnan Jihar Bauchi, domin babban abin da na ki jini a rayuwata shine in ga matasa sun lalace suna shaye-shaye da kuma zaman banza babu Sana’a. Domin ni tun tasowata ban zauna haka ba, kuma tun da mijina ya zama Sanata, ya zama minista har ya zama gwamna, ban taba ruduwa na zauna bana Sana’a ba.”

Kofata A Bude Ta Ke Ga RAYAAS – Kakakin Majalisar Bauchi

Haka shi ma a jawabinsa, Kakakin Majaliasar Dokoki na Jihar Bauchi, Hon. Abubakar Suleiman Dangaladiman Ningi ya bayyana kungiyar RAYAAS a matsayin wacce ta dace da zamani wajen amfanar da al’ummarmu ta yau, “Babban abinda ya birge ni shine yadda ku ka gayyaci kwararru a fannoni daban-daban da kuma mu ‘yan siyasa don ilmantar daku abubuwan da zasu amfane ku.”

Kakakin ya kara da cewa kofarsa a bude ta ke ga wannan kungiya a kowane lokaci don aiki tare wajen inganta wannan al’ummar tamu mai albarka. Sannan ya ja hankalin kungiyar da ci gaba da bin doka da oda a dukkan al’amuranta.

Haka shi ma a cikin jawabinsa, Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Shehu Na Amo Dange ya karanta tarihin kafuwar kungiyar da yadda ta samu rajista da kuma dukkan tsare-tsarenta da adireshin babban ofishinta dake Kaduna da sauran rassa. Haka kuma ya gode wa Uwargidan Gwamnan Bauchi da Kakakin Majalisar Bauchi, da wakilin Mai Martaba Sarkin Bauchi da sauran manyan baki da suka samu damar halartar taron.

Kazalika Uban Kungiyar na Bauchi, Alhaji Danlami Baban Takko, Falakin Dass ya ja hankalin ‘ya’yana kungiyar da kama Sana’a musamman mata, yana mai cewa su bude gidajen sayar masa da kuma shagunan wanki da guga, yana mai cewa Uwargidan Gwamna da Kakakin Majalisa zasu tallafa masu.

An gabatar da takardu daban-daban da suka hada da Farfesa Khalid Abdullahi na Jami’ar Ahmadu Bello wanda ya gabatar da takarda akan “Tasirin Kungiyoyin Matasa A Tsakanin Al’umma”

Sai kuma Barista Aliyu Bin Idris, akan

“Gudummuwar Matasa Ta Bangaren Addini Da Cigaban Zamani” sai takardar da Malam Umar Mohammed Gombe ya gabatar akan “Tasirin Matasa Ta Fuskar Adabi” sannan an gudanar da wasannin dabe don nishadantar da mahalarta taron.

A karshe Shugaban Kungiyar RAYAAS na Jihar Bauchi, Aliyu Mukhtar Yakubu da kuma Shugabar Mata ta Jihar Bauchi, Hajiya Fati Charisma suka jagoranci manyan baki, inda suka kewaya da su ga kayayyakin sana’o’in hannu da ‘ya’yan kungiyar mata suka sarrafa da hannunsu da suka hada da kayan yara, dardumar daki, kayan sanyi, tuma kasa, takalma da sauransu, inda Uwargidan Gwamna ta kaddamar da su.

Haka zalika jim kadan bayan kammala taron, ‘ya’yan kungiyar da shugabanninsu sun kai ziyarar musamman zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Gidan Babban Limamin Bauchi, Gidan Limamin Masallacin Gwallaga sannan da Gidan Tsohon Firaminista, Marigayi Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa da Kabarinsa

Bauchi 2019: Sakonni Guda Biyar A Takaice

Daga Auwali Adamu Differences

Godiya:

Da farko muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya bamu ikon gudanar da wannan gagarumin taro cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

Yabon Gwani ya zama dole, wajibi ne mu godewa daukacin shugabanni da membobin kungiyar RAYAAS ta kasa, musamman shugabanni da membobin kwamitocin shirya wannan taro na kasa da na jaha, da membobi da shugabanni kungiya reshen jahar Bauchi bakidayansu, da malaman da su ka fadakar da mu a wannan taro, da manyan bakin da su ka samu damar halarta, sannan da sarakuna uwayen kasa da malaman da mu ka ziyarta, ‘yan jarida, jami’an tsaro, da dukkanin al’ummar jahar Bauchi bakidaya, da duk wanda ya tamaka ta kowace hanya, muna godiya, hakika kun yi matukar kokari Allah Ya saka muku da alkairi kuma ya biya ku da gidan Aljanna da mu bakidaya.

Jaje:

Sannan zan yi amfani da wannan dama wajen jajantawa shugabannin kungiya reshen jahar Nasarawa da Benue da su ka hadu da tsautsayi na hadarin mota akan hanyarsu ta komawa gida. Muna rokon Allah Ya ba su lafiya kuma ya kare na gaba.

Bangajiya:

RAYAAS tamu ce bakidaya, saboda haka dole sai mun hada kai wajen ciccibata zuwa mataki na gaba, don haka kofa a bude ta ke ga masu niyyar bada shawara ko gyara ta hanyar da ta dace.

Za ku iya tura sako kai tsaye (ta pribate) zuwa ga shugaban babban kwamiti na musamman wato, Alh. (Dr) Adam MG Dangambo akan wannan lamba; 08063174949. Ko Sakataren Kwamiti, Malam Umar Mohammad Gombe; 08030503722. Mun gode.

SendShareTweetShare
Previous Post

Nazarin Kan Masana’antar Kannywood A Shekarar 2019

Next Post

Barka Da Sabuwar Shekara: Taya Kiristoci Murna Abin So Ne!

RelatedPosts

Barebari

Barebari Da Al’adunsu Na Aure

by Umar Mohammed Gombe
1 month ago
0

Gabatarwa: Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan...

Al’adun Auren Zawarawa A Kasar Hausa   

Al’adun Auren Zawarawa A Kasar Hausa  

by Umar Mohammed Gombe
5 months ago
0

Ma'anar Al'ada Kalmar Al'ada ta sami ma'anoni daga masana daban-daban....

Mawaka Da Kidan Gargajiyar Hausa

Mawaka Da Kidan Gargajiyar Hausa

by Umar Mohammed Gombe
7 months ago
0

Wannan wani guzuri ne da na ci karo da shi...

Next Post
Barka Da Sabuwar Shekara: Taya Kiristoci Murna Abin So Ne!

Barka Da Sabuwar Shekara: Taya Kiristoci Murna Abin So Ne!

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version