Connect with us

Uncategorized

Na Yafe Wa Wadanda Suka Yi Wa Gidana Kawanya –Clark

Published

on

Tsohon Ministan kasarnan, Edwin Clark ya ce, ya yafe wa wadanda suka kai mamaya a gidansa bisa zargin yana boye makamai.
Clark, ya yi wannan bayanin ne a sa’ilin da Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya ziyarce shi a Abuja.
A ranar 4 ga watan Satumba ne ‘yan sanda suka gudanar da binciken kwakwaf a gidan na Clark, bisa zargin sa da boye makamai.
Clark ya ce, ya yanke shawarar yafe masu ne saboda samar da zaman lafiya a kasar nan, duk da yake su kansu ‘yan sanda sun ba shi hakuri a kan binciken gidan na shi.
“Na manta da duk abin da suka yi mani, saboda Shugaban ‘yan sandan na kasa ya ba ni hakuri a kan hakan, ta hanyar wata kakkarfar tawaga da ya turo. Na yafe masu saboda dorewar kasarnan.
“In ban yafe ba, tabbas akwai mutane da ke shirye da daukan matakin rigima, ba na kuwa son a yi rigima da sunana.
“Na kuma roki matasa na, ‘ya’yana da suka taru a Yenagoa, Jihar Bayelsa, ransu a bace da hakan, na ce su zauna lafiya,” in ji Clark.
Clark ya ce, an shirya abin ne da nufin kaskantar da gwamnatin da Shugaba Buhari, ke jagoranta.
Clark ya ce, “Ba matsala ne ba a zo a binciki gidana, amma in an yi hakan ne domin a kaskantar da ni da kuma gwamnati, lallai akwai matsala.
“Duk abin da ka yi, in har ba ka yi shi da kyau ba, zai iya shafan gwamnatin Shugaba Buhari, kamar yadda in ka yi shi da kyau ma hakan.
Clark ya ce, ai hankali ma ba zai dauka ba, a ce a shekarunsa da matsayinsa yana tara makamai.
Ya kara da cewa, bai dace a tsammaci tsoho dan shekaru 91, wanda ya cinye rayuwarsa yana yakin neman a zauna lafiya a kasarnan, ya kuma umurci matasa da su ajiye makami, sannan a zo ana zargin sa da tara makamai ba.
Clark ya ce, ya rubuta wa Shugaban kasa, yana neman sa da ya sanya a binciki lamarin da kyau da wadanda suka sanya a yi hakan, domin bai kamata a bar su, su sha da hakan ba.
Tun da farko, Sanata Shehu Sani, ya ce ya ziyarci gidan na Clark ne domin ya nu na masa damuwarsa a kan abin da ya faru din.
“Na ji dadin jin cewa su kansu ‘yan sandan sun nemi gafaran hakan.
“Ina kira a gare ka, a matsayinka na Uba, ka amshi hakurin da ‘yan sandan suka ba ka, ka kuma yi duk mai yiwuwa wajen nu na matsayarka, domin kar wasu su fake da hakan su tayar da hankali.
“Ku ne tushen tarihin kasarnan, ka san abin da ya faru a jiya, ka na kuma sane da abin da ke faruwa a yau din nan, har yanzun kuma muna da bukatar ka domin dorewar kasarnan,” in ji Sanata Shehu Sani.
Sanata Sani, sai ya gargadi hukumomin tsaro da su rika yin taka-tsantsan da rahotannin da suke yin aiki da su.
“Ya kamata hukumomin bincike na sirri da sauran hukumomin tsaro duka, su rika bibiyan mutanan da suke kawo ma su duk wasu bayanai, domin su guje wa zubar da kimar su da ta gwamnati.
“Na yi imanin a matsayinka na Uba, za ka dauki wannan abin da ya faru, cewa ya faru ne ba tare da sani ko nufin wanda ke jagorancin kasarnan ba.
“Amma na san mahimmancin bukatar yin bincike a kan lamarin, domin ko ba komai, kar mu zargi wasu, alhalin wadanda suka kitsa lamarin suna can boye.
“Wannan abin da ya faru a gidanka, shi zai zama farko, kuma shi ne karshen yin amfani da masu kawo bayanan karya domin a ci mutuncin mutanan kirki.
“Ka yi duk abin da ya kamata na ganin dorewar zaman lafiya da hadin kan kasar nan, ya kamata a yaba da hakan.
“Ba na shakkan an yi hakan ne domin zubar da kimar gwamnatin Shugaba Buhari, a kuma hada shi fada da mutanen da suke ganin kimar sa,” in ji Shehu Sani.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: