Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya bayyana cewa yayi takaicin rashin samun damar buga wasannin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da zata fafata da Liverpool a tsakiyar satin nan.
Tuni dai aka bayar da rahoton cewa mai tsaron bayan, Sergio Ramos ba zai samu damar buga wasa a karawar kungiyar ta sa karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai da za ta kara da Liverpool ba, saboda raunin daya samu a kafarsa.
Sanarwar da Real Madrid ta fitar ta ce Ramos mai shekaru 35 ya samu raunin ne lokacin da ya ke bugawa kasarsa kwallo a wasannin neman gurbin shiga gasar EURO da suka gudana a takaitaccen hutun tsakiyar kaka da ‘yan wasa suka samu.
Real madrid na shirin karawa da Liverpool ne ranar 6 ga watan nan a zagayen farko na wasan gab dana kusa da karshe na cin kofin zakarun turai gabanin su sake haduwa a wasa na biyu ranar 14 ga watan.
Jaridun wasannin Spain sun ruwaito Ramos na cewa raunin ya matukar harzuka shi ganin yadda zai rasa haduwar ta cin kofin zakarun Turai da kuma wasan El Classico duk dai a cikin wannan watan wato haduwar Barcelona da Real Madrid.
A shekarar 2018 ne Real Madrid ta yi nasara kan Liverpool bayan zura mata kwallaye 3 da 1 baya ga targada hannun tauraron tawagar wato Mohamed Salah da Ramos ya yi a wancan lokaci dalilin da ya sanya wasu ke kallon haduwar a matsayin ta huce haushi duk da cewa Liverpool din ta yi nasarar dage kofin a shekarar 2019.
Dukkanin kungiyoyin biyu dai na fama da tarin majinyata wanda ya haddasa musu koma baya a wasanninsu na wannan kaka musamman Liverpool data rasa babban dan wasanta na baya, Virgil van Dijk.