Abba Ibrahim Wada" />

Na Yi Bakin Cikin Rashin Zuwa Wasan Karshe —Wenger

LONDON, ENGLAND - MAY 07: Arsene Wenger, Manager of Arsenal reacts during the Premier League match between Arsenal and Manchester United at the Emirates Stadium on May 7, 2017 in London, England. (Photo by Richard Heathcote/Getty Images)

 

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa yayi bakin ciki sosai sakamakon rashin nasarar da suka yi a hannun kungiyar Atletico Madrid a gasar Europa.

Wenger ya ce abin bakin ciki ne da takaici a ce ya bar Arsenal ba tare da wata gasa ba kuma yana bakin cikin rashin nasarar da suka yi a ranar ta Alhamis sai dai ya ce za ije ya zauna domin ya huce daga bakin cikin da yake damunsa.

Atletico Madrid ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa, bayan da ta ci Arsenal 1-0 a Spaniya a ranar Alhamis.

Atletico ta buga kunnen doki 1-1 da Arsenal a filin wasa na Fly Emirates, inda ta ci 1-0, jumulla ta ci kwallo 2-1 karawar da suka yi gida da waje kenan.

A karshen kakar nan Arsene Wenger zai bar Arsenal, bayan shekara 22 da ya yi yana jan ragamar kungiyar, kuma bai taba cin kofin Zakarun Turai ba.

Atletico ta lashe Europa karo biyu a tarhi, za kuma ta buga Champions League a babi, tana ta biyu a kan teburin La Liga da maki 75, saura wasa uku a kammala gasar Spaniya ta bana.

Ita kuwa Arsenal karo biyu kenan a jere ba za ta gasar Zakarun Turai ta badi ba, domin tana ta shida a teburin firimiya shekarar nan.

 

Exit mobile version