Connect with us

SIYASA

Na Yi Kyakyawar Shiri Don Kawo Canji A Salon Mulkin Kasar Nan –Danmaliki

Published

on

Daga Ibrahim Muhammad, Kano.
An bayyana cewa mulkin da jam’iyyar PDP ta yi a kasar nan na shekaru 16 ta watsar da lalitar kasa ba abin da aka yi na amfanar al’umma wannan ta sa ba zai yi wu ace Shugaban kasa Muhammad Buhari ya iya kammala gyaran da ya dauko na kasarnan a cikin wa’adin zango daya ba, kamata ya yi ace ya samu damar yin zango uku don inganta ci gaban kasar nan. Me neman takarar tsayawa wakilcin kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa a inuwar jam’iyyar APC Alhaji Abdulhalim Abdullahi Liman Danmaliki ya bayyana haka da yake zantawa da wakilimmu a Kano.
Ya ce, idan Shugaba Buhari ya koma a karo na biyu zai dora a kan abin da ya soma na inganta tsaro da gina kasarnan da hana wawushe dukiyar kasar nan da wasu ‘yan tsiraru suke. Zuwansa ya dora ayyuka da tun PDP aka fara amma ba a yiba irinsu layin jirgi da yazo ya kammala da sauran ayyuka.
Ya kara da cewa idan aka daure wa wahalarda ake ciki a halin yanzu da gwamnatocin baya suka sanya kasar nan, idan Buhari ya dora a karo na biyu za’a sami sauki da daidaitar al’amura dan haka ya kamata a sake ba shi goyon baya don dorawa a kan tsare-tsare da yake bijirowa dasu.
Alhaji Abdulhalim ya ce, gwamnatin Ganduje a jihar Kano tana kokari wajen ci gaban Kano har karramawa shi a kayi a kan kulawa da yake kan ci gaban ilmi. Sannan zuwansa ya dora a kan aiki daya gada na asibitoci ya ginasu ana aiki a cikinsu da sauran ayyuka masu amfani da yake daya kamata a ci gaba da mara masa baya a zabe mai zuwa don ci gaban jihar Kano.
Alhaji Abdulhalim Liman DanMaliki ya ce, neman takarar majalisar tarayya da yake na Gezawa da Gabasawa ta samo asali ne duba da irin gudummuwa da mahaifinsa Alhaji Abdullahi Liman Danmaliki ke bayarwa a cikin al’umma duk da shiba ma’aikacin gwamnati bane ko kuma dan siyasa amma ya yi shimfida ta alheri ta lallafawa al’umma.
Wannan tasa mutane suka ga zaifi kyau su dauko dansa su shigar da shi siyasa don samun dama a gwamnati da za a dora sosai a kan abin da ake musu musamman ma da yake suna ganin rashin amfanin wakilci da suka tura ake musu a majalisar tarayya.Wadanda aka tura basu da mai fada musu gaskiya amma shi saboda mahaifinsa da irin da irin kimarsa da kuma sauran jama’a da in sukaga wani abu na gyara za su kirasa su nuna masa.
Abdulhalim ya ce shi bai taba shiga wata harkar siyasa ba sai yanzu amma ana mu’amala ta yau da kullum da jama’a ana kyautata musu yana wakiltar mahaifinsa a harkokin tallafa wa ci gaban al’umma duk gudummuwa da mahaifinsa ke bayarwa samada shekaru 20 ya zama ruwan jakara wanda al’ummar Gezawa da Gabasawa da jahar Kano ke dandana.
Yace kujerar majalisar wanda yake kanta a yanzu ba inda aka taba gani ya mike a majalisa ya kawo kuduri na al’ummarsa sannan duk inda aka shiga a yankunan akwai matsaloli.Sannan irin damarda ake samu na daukar ayyuka ga matasa ba’ayi idan ma ana samu sai a karkatar wani wajen ba mazabarsu ba.
Alhaji Abdulhalim Liman Danmaliki ya yi kira ga masu zaben fidda Gwani a kan suji tsoron Allah a matsayinsu na wakilai na jama’a hakkin mutane ne a kan su su duba a cikin yan takara su zabi cancanta kar su bari wani ya ba su kudi dansu zabeshi su duba cancanta saboda Allah zai tambayesu duk abin da suka yi akwai hakki a kansu,su kuma al’umma su duba cancanta su yi abu tsakani da Allah su zabi wanda zai zo ya taimaki ci gaban jama’a.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: