Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

A Na Zaman Ɗar-ɗar Tsakanin Amurka Da Turkiya

by
5 years ago
in KASASHEN WAJE
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Taƙaddamar da ta kunno kai tsakanin Amurka da Turkiya na haɓaka inda yanzu ƙasashen biyu ke zaman ɗar- dar da juna kuma duniya na fargabar in lamarin ya ci gaba har na wani tsawon lokaci yana iya haifar da illa mai muni.

Ana ci gaba da zaman ‘dar-‘dar ne, inda Tukiyya ta dakatar da bai wa yawancin Amurkawa Biza, domin ramuwar gayya kan makamancin abin da Amurkar ta yi wa ƙasar.

Sai dai ramuwar gayyar ta soma jefa harkokin kasuwancin Turkiyya cikin wani hali, abinda ake fargabar zai iya haifar da illa mai muni ta wani lokaci mai tsawo.

Labarai Masu Nasaba

Jami’an Tsaro Sun Yi Ruwan Tiyagas Kan Musulmai A Sahun Sallar Idi A Ethiopia

Mutum 8 Sun Mutu, 43 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Saudiyya

Da yake gargaɗi kan wannan abu dake faruwa, masanin kimiyyar siyasa Cengiz Aktar ya ce, “wannan wani abu ne da ba a taɓa gani ba, ko da kuwa lokacin da ƙasashen suka sami saɓanin da ya fi haka muni, ba a taɓa ganin an shiga irin wannan halin ba, lamarin ba abin wasa bane.”

Jayayyar dai ta samo asali ne tun makon da ya gabata lokacin da aka kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka mai suna Metin Topuz, ana tuhumarsa da laifin ta’addanci. Lauyoyin Turkiyya sun zargi Topuz da alaƙa da babban malamin nan da yanzu haka ke zaune a Amurka, Fethullah Gulen, wanda aka zarga da laifin kitsa makircin juyin mulkin da bai samu nasara ba a shekarar da ta gabata.

A jiya ne ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gayyaci mataimakin babban shugaban ofishin jakadancin Amurka inda aka buƙaci Amurka da ta dakatar da matakin da ta ɗauka na hanawa ‘yan Turkiyya Biza.

Akwai alamun za a ci gaba da samun zaman ɗar-ɗar tsakanin ƙasashen biyu, bayan da ofishin lauyan gwamnatin Turkiya ya bayyana sake karɓo izinin kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka dake Istanbul, kuma jami’an tsaro sun riƙe matar ma’aikacin da ake son kamawa da ɗansa.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Barin Takarar 2019 A Arewa: Ƙusoshin PDP Sun Yi Wa Abuja Ƙawanya

Next Post

Ƙasar Iran Ta Ja Kunnen Amurka

Labarai Masu Nasaba

Jami’an Tsaro Sun Yi Ruwan Tiyagas Kan Musulmai A Sahun Sallar Idi A Ethiopia

Jami’an Tsaro Sun Yi Ruwan Tiyagas Kan Musulmai A Sahun Sallar Idi A Ethiopia

by Khalid Idris Doya
2 weeks ago
0

...

Mutum 8 Sun Mutu, 43 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Saudiyya

Mutum 8 Sun Mutu, 43 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Saudiyya

by
4 weeks ago
0

...

Jirgin Ruwan Yakin Rasha Ya Dulmiye Cikin Tekun Black Sea

Jirgin Ruwan Yakin Rasha Ya Dulmiye Cikin Tekun Black Sea

by
1 month ago
0

...

Isra’ilawa Sun Zargi Falasdinawa Da Kai Farmaki Kan Kabarin Annabi Yusuf

Isra’ilawa Sun Zargi Falasdinawa Da Kai Farmaki Kan Kabarin Annabi Yusuf

by Muhammad Bashir
1 month ago
0

...

Next Post

Ƙasar Iran Ta Ja Kunnen Amurka

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: