Connect with us

SIYASA

Nada Gawuna Mataimakin Gwamnan Alheri Ga Jihar Kano -Hajiya Uwa

Published

on

Mataimakiya ta musamman ga Gwamna Ganduje a ofishin Kwamishiniyar al’amuran Mata ta jiharKano.Hajiya Uwa Matar Dansanda ta bayyana nadinda Gwamnan Kano ya yi wa Kwamishinan ma’aikatar Gona Alhaji Dokta Nasir Yusuf Gawuna da cewa alkhairi ne ga ci gaban jihardomin kuwa an ajiye kwarya a gurbinda ta dace.

Ta ce duba da irin kyakkyawar mu’amala da take wanzuwa tsakaninsa da al’ummar jihar Kano wanda duk lokacin da ka same shi yana haba-haba da mutane da ba su kima kullum hakan ke kara masa masoya.

Hajiya Uwani Matar Dansanda ta kara da cewa, wannan matsayi da aka bai wa Gawuna ta kara wa Gwamna Umar Ganduje kwarin gwiwa na  sake cin zabe da gagarumar nasara dar bisa dari saboda  wadanda  ma basa jam’iyyar APC  za su zabeta saboda alakarsu da Gawuna.

Ta kara da cewa, Mataimakin Gwamnan Alhaji Dakta Nasir Yusuf Gawuna  mutum ne da yake harkokin siyasarsa tun daga tushe kowa yasan irin dawainiyar da ya rika yi  ta kawo ci gaba a karamar hukumar Nasarawa lokacin da ya yi shugabancin karamar hukumar ya gina al’umma ya kuma samar da ayyukan ci gaba. Irin alkhairin da ya shuka na dadadawa da farantawa al’umma ita take bin sa, yake samun ci gaba a harkokinsa na siyasa.

Matar Dansanda ta ce, a kwamishinan da yake na ma’aikatar Gona ya riki amanar Gwamna wajen cika burin Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na inganta da habaka harkar noma a kasar nan, wanda a jihar Kano da irin jajircewa da aiki tukuru da kwazon Gawuna harkokin noma yana ci gaba da habaka a jihar nan.

Ta ce da yake Gwamna Ganduje Jagorane mai kyakkyawan tunani da hangen nesa da sanin ya kamata ya duba yaga nagartar Kwamishinan da irin gudummuwar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar Kano ya dauko wanna matsayi ya bashi da take yi masa fatan alkhairi.

Mataimakiyar ta musamman ga Gwamnan Kano a kan Yara a ma’aikartaral’amuran Matan Hajiya Uwani ta yaba wa mai dakin Gwamna jihar Kano Hajiya Dokta Hafsat Umar Ganduje a kan irin gudummuwar da take bayar wa da ita da ya’yanta wajen ganin ci gaban jihar Kano a fannoni daban-daban na gina rayuwar al’umma musammanma wajen ganin an kawo ci gaba ga Mata da Matasa da kananan yara musamman marayu
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: