Nada Matattu A Gwamnatin Tarayya Abun Kunya Ne Ga Buhari –Jam’iyyar APDA

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wata jam’iyyar siyasa a Nijeriya (APDA) ta jefa wa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari tambaya kan cewar ta yaya aka yi har ya yi sake wajen nada matattu domin su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya, inda jam’iyyar ta ce kurakurai suna dankare a cikin nadin mukaman siyasar na Buhari.

Jam’iyyar ta ce kuskuren da aka samu wajen nadi mukaman abun kunye ne ga kasar Nijeriya da kuma nuna nakasu ga dukkanin jama’an da suka ga sanawar jerin jadawalin sunayen shuwagabanin da za su jagoranci hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayyar.

Jam’iyyar sun dai ta bayyana cewar mutane tara ne aka samu sun rigaya sun mutu a cikin jerin sunayen da Buharin ya fitar da su shugabanci sashin hukumomin da kuma wasu ma’aikatu da sashi-sashi na gwamnatin tarayya.

Jam’iyyar ta APDA ta yi wadanan jawaban ne a cikin wata sanarwar manema labaru wacce suka raba ta a jiya Lahadi wacce babban sakataren watsa labaru na jam’iyyar Tosin Adeyanju ya sanya wa hanu, ya kuma baiwa shugaban Nijeriya Buhari shawarar gami da yin kiresa da ya bayar da umurni wa wadanda abun ya shafa domin su dawo da martabar tsarin fidda jadawalin domin kaurace wa aikata abun kunya a idon duniya da kuma abun kunya a cikin kasa.

Ya ce, sun zura ido su ga jerin sunayen da Buharin zai fitar domin suna tsammanin za a fito da hazikai, jajirtattu kuma mutane masu nagarta daga cikin Nijeriya wadanda za su yi aiki tukuro domin ciyar da Nijeriya gaba ba wai fiddo da matattu ba.

Sun kuma bukaci Buharin da ya daina bayar da dama wajen jawo wa Nijeriya abun kunya da takaici a idon duniya, ya kuma hori gwamnatin tarayya take nutsuwa sosai wajen tafiyar da aiyukansu.

A ranar juma’ar nan ne dai shugaban Nijeriyan ya amince da nade-naden mukaman shuwagabanin da za su jagoranci sashi-sashi na wasu hukumomin da ma’aikatun gwamnatin tarayya, inda a cikin sunayen ka samu matattu a cikin jadawalin.

Wannan yanayi mai ban mamaki da ta’ajibi, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya nada wasu matattu a matsayin jagorori da mambobi na wasu hukumomin gwamnatin tarayyar kasar, to amma a wata majiya ta shaida ma na cewa, hakan ya faru ne sakamakon dadewa da sunayen su ka yi a ajiye ba tare da ya sanya mu su hannu ba, sakamakon jinya ya yi fama da ita a wajejen karshen shekarun baya.

Wannan kuskuren dai na ci gaba da jawo cecekuce a fadin Nijeriya, inda kuma gwamnatin ta bukaci ministoci su bayar wa sabbin nada-naden izinin fara aiki nan take, jadawalin dai ya fito ne daga babban sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a ranar juma’ar.

Exit mobile version