Daga Sabo Ahmad, Zariya
Shugaban kungiyar shugabannin rikon kananan hukumomi ta jihar, kuma shugaban riko na kakamar hukumar Kumbotso, Baba Sharu Dala, ya bayyana cewa, rushe shugaannin kanannan hukumomi wadanda wa’adinsu ya kare, da maye gurbinsu da shugabannin riko na yanzu, na nuna yadda mulkin dimokaradiyya ya samu nasara a jihar Kano.
Shugaban ya ci gaba da cewa, labaran da suke samu daga kananan hukumomin dangane da yadda shugabannin rikon ke tafiyar da mulkinsu abin farin ciki ne, bisa kokarin da suke na kyautata alakarsu jama’ar da suke mulka, ta hanyar tabbatar da adalci.
Sharu Dala, ya kara da cewa, kokarin da shugabannin rikon ke yi, na da nasaba da aiwatarda kyawawan manufofin gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na yi wa al’ummar jihar ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma.
A karshe, ya nuna wa shugabannin rikon kanananan hukumomin da su dauki yabon da jama’a ke yi musu a matsayin karin karfin gwiwa, wajen ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar, kamar yadda koyaushe gwamna ke umarni da a yi.