Refeal Nadal dan kasar Spain ya lashe kofin gasar kwallon tennis ta US Open, da aka kammala a birnin New York na Amurka, a wasan karshe da suka fafata da Kebin Anderson mai wakiltar kasar Afrika ta Kudu.
Nadal ya lallasa Anderson da kwallayen 6-3, 6-3, da kuma 6-4. Kuma karo na uku kenan da Nadal ke lashe kofin gasar US Open.
Wannan nasara ta bai wa Nadal damar lashe kofunan gasar ta Grand Slam daban daban har biyu a jere cikin wannan shekara daya, domin kuwa hi ne ya lashe kofin gasar French Open da ta gudana a watan Yuli.
Gasar kwallon tennis da ake kira Grand Slam dai ta kasu kashi hudu, wato US Open, French Open, Australian Open da kuma Wimbledon.
Pete Sampras na Amurka a matsayi na 3 da kofunan Grand Slam din 14, sai kuma Nobak Djokobic na kasar Serbia mai rike da kofunan gasar har guda 12.