Abba Ibrahim Wada" />

Nadal Zai Kece Raini Da Federer A Yau

Roger Federer da a shekara da ta gabata ya samu nasarar komawa matsayinsa na lamba daya mafi kwarewa a fagen wasan kwallon Tennis ajin maza a duniya zai fafata da Rafael Nadal a yau Asabar a wasan dab da na karshe a gasar Rolland Garros.

Federer dan kasar Switzerland na samun goyan baya daga sassa daban-daban ganin kwarewar sa a duniyar Tennis,sai dai Rafael Nadal ba kanwar lasa bane domin ya doke shi a wasanni da dama da suka fafata a shekarun baya.

Federer ya kafa tarihin zama dan wasan Tennis na biyu a duniya da yafi takwarorinsa yawan lashe kofunan wasannin Tennis, bayan Jimmy Connors dan kasar Amurka da ya lashe kofunan gasar tennis har sau 109, a tsawon lokacin da ya shafe a fagen wasan na tennis.

Rafael Nadal na daga cikin ‘yan wasa da ya kafa tarihi a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa inda ya lashe kofin gasar sau 10 sai dai Nadal ya ce yana cike da farinciki kasancewa zai fafata da Roger Federer a wannan gasa ta Rolland Garros.

A bangaren mata, a yau Sabar ‘yar kasar Austria Ashleigh Barty zata fafata da ‘yar kasar Amurka Amanda Anisimoba,karawa ta biyu zata hada ‘yar Birtaniya Johanna Konta da ‘yar kasar Tchekue Marketa Bondrousoba.

Exit mobile version