Nadin Kwamishinonin INEC: Wasu Sun Samu, Wasu Ta Leko Ta Koma 

Daga Muhammad Maitela,

Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da nada wasu sabbin Kwamishinoni Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) guda biyar, yayin da kuma ta leko ta koma wa wasu sakamakon fatali da amincewa da nadinsu a da’irar shugabancin hukumar.

Daga cikin wadanda ta leko ta koma wa, akwai Misis Lauretta Onochie, ‘yar asalin Jihar Delta, wadda fadar shugaban kasa ta gabatar ga zauren, da ake ta ka-ce-na-ce a kanta saboda zargin ‘yar Jam’iyyar APC ce mai mulki, duk kuwa da cewa ta fito fili ta musanta hakan a yanzu. Haka kuma majalisar ta kuma jingine nadin Farfesa Sani Muhammad Adam daga arewa ta tsakiya har sai kwamitinta na INEC ya gama bincike a kansa.

Zauren ya sanar da hakan a takardar manema labarai mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban majalisar kan harkokin yada labarai, Mista Ezrel Tabiowo.

Sanarwar ta yi karin bayanin cewa tantancewa tare da nada kwamishinonin ta biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar ne a kan hukumar zabe.

Wadannan kwamishinonin da majalisar ta amince da nadinsu su ne:Farfesa Abdullahi Abdu Zuru (Arewa Maso Yamma), Farfesa Muhammad Sani Kallah (Katsina), Farfesa Kunle Cornelius Ajayi (Ekiti), Dakta Baba Bila (Arewa Maso Gabas), kana da Saidu Babura Ahmad (Jigawa).

Da yake mika rahotonsa, shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Gaya, ya ce kwamitinsu ya samu takardun korafe-korafe da dama a kan nadin Misis Lauretta Onochie da Farfesa Sani Muhammad Adam, wanda hakan ya jawo daukar matakin yin fatali da batun.

Har ila yau, shugaban kwamitin, Sanata Gaya ya kara da cewa, korafe-korafen sun zargi Misis Lauretta da shiga harkokin siyasa tare da kasancewa mamba a jama’iyar siyasa.

Haka zalika, ya ce nada ta a matsayin shugabar INEC ya saba wa tsarin raba daidai na mukaman gwamnatin tarayya, wanda kuma yanzu haka akwai kwamishiniyar INEC, Barista Mary Agbamuce-Mbu, wadda ‘yar asalin jihar Delta ce da tuni majalisa ta amince da nadin ta.

A batu na daban kuma, Sanata Gaya ya ce kwamitin ya dauki wannan matakin ta hanyar dogara da sashi na 14, karamin sashi (3) na kundin tsarin mulki wajen kin bayar da shawarar amincewa da Misis Onochie.

Har ila yau, kwamitin ya bukaci zauren majalisar ya jingine batun amincewa da nada Farfesa Sani Muhammad Adam, har sai kwamitin ya kammala binciken da yake gudanarwa kan korafe-korafen da aka gabatar masa dangane da nadin nasa.

Exit mobile version