NAF Gudanar Ta Faretin Girmamawa Ga Tsohon Babban Hafsanta

NAF

Daga Mahdi M. Muhammad,

A wani vangare na ayyukan mika ragamar shugabanci tsakanin Babban hafsan sojin sama na 20 a tarihin sojin saman Nijeriya (NAF), da na 21, NAF a ranar, 2 ga Fabrairu 2021, an gudanar da kyakkyawan taron ne a sansanin NAF da ke Abuja don karrama Air Marshal Sadikue Abubarkar (Mai ritaya) don nuna alamar ficewarsa daga aikin.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, a yayin taron, Shugaban mai ritaya ya bukaci ma’aikatan NAF da su ci gaba da jajircewa a yakin da ake yi na dawo da zaman lafiya a sassan kasar da ke fama da rikici tare da umartar su da su ci gaba da ba da mafi kyawun abin da suka yi wa kasa.

Da yake ci gaba da magana, Air Marshal Abubakar ya nuna kwarin gwiwa kan kwarewar sabon shugaban, Air Vice Marshal (AVM) Oladayo Amao, don daukar NAF zuwa babban matsayi. Ya kuma bukaci sabon shugaban da ya himmatu don dorewar kudurorin inganta ayyukan da Gwamnatinsa ta sanya a cikin shekaru 5 da suka gabata. A cewarsa, “A cikin shekaru 5 da suka gabata, mun sami damar sake fasalta da sake sanya NAF cikin kwararru kuma masu da’a. Tutar NAF a yau tana fifilawa daga Agatu zuwa Gembu da kuma zuwa Gusau, Katsina, Daura, Owerri, Birnin Gwari, Ipetu-Ijesha, Kerang, Gombe da Bauchi ”.

sohon shugaban ya kara da cewa, tsarin da ake da shi a yanzu tabbas zai kara wa hukumar NAF kima wajen tabbatar da Nijeriya da kuma mutanen ta. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, da sanadin isowar karin jirage 15 da jirage marasa matuki na ‘Unmanned Combat Aerial Vehicles’ (UCAVs) guda 8, za a samarwa hukumar da kayan aikin ya dace wajen magance matsalolin tsaro da ke damun kasar. Air Marshal Abubakar ya jaddada cewa NAF za ta iya yin amfani da karfin sama ta yadda ya dace, yadda ya kamata kuma a kan kari a dukkan wuraren yaki da ake gudanarwa a duk fadin kasar.

Yayin da yake bayar da labarin wasu nasarorin da ya samu, tsohon shugaban ya nuna cewa, rundunar ta hanyar kokarin gina iyawa ya horar da jami’ai 133, wadanda a cewarsa, sune kashi 49 cikin dari na dukkan matukan jirgin NAF masu aiki a vangarori daban-daban na rikice-rikice don tabbatar da kasar.

Ya kara da cewa, karin matukan jirgin sama guda 21 za su kammala horon su kafin karshen zango na farko na 2021, don shiga sahun abokan su a yakin kare martabar yanki da kuma ikon kasa. Air Marshal Abubakar ya kuma bayyana cewa, yayin da yake kan karagar mulki, ya samu nasarar aiwatar da wani shiri na dinke varakar dake tsakanin tsinkayen karfi da kariyar karfi, kamar yadda ya ce, rundunar ba za ta iya aiwatar da ikon sama yadda ya kamata idan ba su da hanyar da za a iya kare tushenta, kadarorin sama da iska.

vangaren bincike da ci gaba, Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, NAF ta shiga kawance da jami’o’in Nijeriya 15, in ji shi, sun ci gaba da bayar da gagarumawa wajen magance wasu kalubalen kula da jiragen NAF. Ya nuna gamsuwa kan barin NAF bayan ya cimma burin da ya sanya a gaba. Don haka ya gode wa babban kwamandan askarawan kasar, Shugaba Muhammadu Buhari, mambobin majalisar kasa, musamman kwamitocin Majalisar Dattawa da na Majalisar kan sojin sama, da kuma jami’an sojojin sama maza da mata da suka ba da goyon baya a tabbatar da cewa an daukaka darajar NAF zuwa mataki mafi girma fiye da abin da ya sadu da shi.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban Kwamitin majalisar Wakilai kan sojin sama, Honorabul Abbas Adigun, da Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, shugaban hafsin soji (COAS), Manjo Janar Ibrahim Attahiru, kazalika da wakilan Babban hafsan tsaro da na hafsan sojojin ruwa.

Haka kuma akwai tsoffin Manyan hafsoshin tsaro da na sama, Air Chief Marshal Oluseyi Petinrin da AVM Femi John Femi (Mai ritaya), babban hafsan tsaro, AVM Mohammed Usman, Daraktan ma’aikatar Sojin sama na tsaro, Mista Ashibel Peter Utsu, da shugaban kungiyar Matan jami’an sojin sama (NAFOWA), Misis Elizabeth Olubunmi Amao, da kuma Shugabannin reshe daga hedikwatar tsaro da hedikwatar NAF, Kwamandojin ‘Tri-Service’ da ‘NAF institude’, Shugabannin sojojin sama na Umarnin NAF 6, tare da sauran manyan hafsoshin soji da suka yi ritaya da yawa.

 

Exit mobile version