Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
An ja hankalin rundunar sojin saman Nijeriya(NAF) zuwa ga wani sako da ake yaduwa a dandalin sada zumunta na wani mai suna Olabisi Amoo wanda yake ikirarin yana da dama ta musamman don taimaka wa duk wani mai neman aiki ko karatu a makarantun NAF.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanrrwar da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na sojin sama (DOPRI), Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar kuma yaba wa manema labarai a Abuja, inda yake cewa, wadanan maganganu na rashin kishin kasa da wannan mutumin da aka ambata a baya yake yi da nufin yaudara da damfarar ‘yan Nijeriya da suke bukatar samun damar aiki, badaidai bane.
NAF na sanar da jama’a cewa ba ta yi talla ba kuma ba ta da niyyar fara aiki da malamai saboda yawancin makarantun da ke yaduwa a duk fadin kasar. Ko da kuwa irin wannan bukatar ta taso, NAF ba za a yada ta ta hanyar daidaikun mutane ba, sai dai a sanar da ita da kuma sanar da dukkan ‘yan Nijeriya ta amfani da kafafen yada labarai da dama.