Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

NAF Ta Fara Jigilar Kayan Tallafin Korona Zuwa Kasashen Afirka Ta Yamma

by Muhammad
April 1, 2021
in LABARAI
3 min read
NAF Ta Fara Jigilar Kayan Tallafin Korona Zuwa Kasashen Afirka Ta Yamma
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mahdi M. Muhammad,

Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ta sake nuna mutuntakarta ta dan adam ta hanyar taimakawa wajen kai kayan tallafin kiwon lafiya na cutar korona, wanda kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta bayar tare da tallafin masu ba da gudummawa kamar tawagar Turai, Gwamnatin Jamus, da ‘United Nations Debelopment Programme & Deutsche Gesellschaft Fur Internationale Zusammenarbeit’ (GIZ).

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na sojin sama (DOPRI), Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar kuma yaba wa manema labarai a Abuja, inda yake cewa, kayan tallafin da za a raba wa kasashe 14 na kungiyar ECOWAS, Nijeriya na cikin kasashe wadanda suka fuskancin yaduwar cutar a zango na biyu.

A yayin da take wajen sauko da jigilar kayayyakin agajin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, a ranar 30 ga Maris 2021, Shugabar tawagar ECOWAS kuma mataimakiyar shugaban hukumar ECOWAS, Finda Koroma, ta bayyana cewa, bukatar wadatattun kayan kiwon lafiya ya zama dole ne don ba wa kasashen ECOWAS damar yaki da cutar a yayin dawowar ta a karo na biyu, musamman a Yammacin Afirka.

Ta bayyana cewa, tallafi na farko da kungiyar ECOWAS ta baiwa kasashe mambobin kungiyar wadanda suke matukar bukatar magunguna shine a watan Agusta na shekarar 2020, kuma kokarin ya ba da fa’ida sosai inganta wajen dakile yaduwar cutar.

Ta nuna godiyarta ga Gwamnatin Nijeriya da kuma zakaran kungiyar ECOWAS kan cutar korona, da Shugaba Muhammadu Buhari, kan ba da tallafin kayan aiki ga ECOWAS a cikin jigilar kayayyakin tallafi.

Koroma ta kara da nuna godiya ga yardar NAF na kasancewa a koyaushe don bayar da tallafi a duk lokacin da aka kira ta, ta kuma mika godiyarta ta musamman ga Shugaban sojojin sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, don karramawar da aka yi masu don gudanar da aikin raba kayan zuwa kasashen ECOWAS da ke cikin tsananin bukata.

A jawabinsa a bikin saukar jirgin, Shugaban wanda daraktan ayyuka, Air bice Marshal (AVM) Ayoola Jolasinmi ya wakilta, ya bayyana cewa, NAF ta dauki jigilar kayayyakin a matsayin babbar dama da kuma cancanta ga ayyyukan. Yayin da yake tabbatar wa hukumar ECOWAS na NAF da himma wajen samun nasarar aikin, ya sake jaddada shirin NAF a koyaushe ta cika aikinta na tsarin mulki na taimakon sojoji ga hukumomin farar hula a duk lokacin da aka kira ta.

Kimanin kayan tallafi 4,000kg, wadanda suka hada da kayan bincike na dakin gwaje-gwaje, Kayan kariya (PPEs), kayan aikin kulawa mai karfi da kuma kayan likitanci daban-daban, za a dauke su ta jirgin ‘7 – man C-130 aircraft crew’.

NAF na da tarihin bayar da taimako ta hanyar jigilar sama ga hukumomin farar hula. A watan Maris na shekarar 2020, ta dauke kayayyakin kiwon lafiya ta sama wanda gidauniyar ‘Jack Ma’ ta bayar, wadanda suka kunshi kwalaye 107 na kayan magani da kayan aiki masu nauyin kilogram 1,360.

Haka zalika, a cikin watan Afrilu na shekarar 2020, NAF ta kwashe kayayyakin kiwon lafiya da kayayyakin da Gwamnatin Turkiyya ta bayar daga Legas zuwa Abuja. Kayan kiwon lafiya masu nauyin kusan 4,000 Kg, wanda wani jirgi ‘NAF C-130 Hercules’ ne ya dauke su zuwa ‘Central Storage Facility’ da ke Abuja, a madadin rundunar tsaro ta shugaban kasa da ke yaki da cutar korona.

A daidai wannan lokacin ne kuma aka ga yadda jirgin NAF din ta dauke wasu kwararrun jami’an kiwon lafiya na cibiyar hana yaduwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), daga Congo Brazzaville, inda suka yi tafiya zuwa wani shirin bayar da horo na hukumar lafiya ta duniya kan kula da cutar korona. Wadannan kokarin sun kasance kusa da yawancin jiragen sama na cikin kasa wadanda aka shirya don jami’an ma’aikatar lafiya ta tarayya (NCDC), da sauran jami’ai don saukin motsi a yayin gudanar da ayyukansu.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ganduje Ya Gode Wa Kansila Mai Mataimaka 18 A Kano

Next Post

Sinadarin dan-tsami Ne Sanadiyyar Mutuwa Da Jikkata Jama’a A Kano – NAFDAC

RelatedPosts

NDLEA

NDLEA Ta Sanar Da Fara Kai Farmaki Dakunan Hada Muggan Kwayoyi

by Muhammad
3 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Shugaban hukuamar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa...

Na'urori

Gombe Za Ta Fara Amfani Na’urori Don Tantance Ma’aikatan Bogi

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Khalid Idris Khalid, Majalisar zartarwa ta Jihar Gombe ta...

Gobara

Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar ‘Yan Makaranta 20 Da Gobara Ta Kashe A Nijar

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna kaduwarsa akan...

Next Post

Sinadarin dan-tsami Ne Sanadiyyar Mutuwa Da Jikkata Jama'a A Kano – NAFDAC

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version