Daga Mahdi M. Muhammad,
Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), bagaren dakarun ‘Operation Thunder Strike’ sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga masu yawa a dajin Chikwale da ke yankin Mangoro na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda yake cewa, an gudanar da aikin ne a ranar, 23 ga watan Janairun, 2021, biyo bayan rahotannin sirri na sahihanci da ke nuna yawan ‘yan bindiga a yankin, wanda yake kusan kolimita 20 da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Dangane da haka ne, bayan jerin samfuran tsaro na sama, rundunar ta aika da wata rundunar da ta dace da jiragen saman yaki masu saukar ungulu don kai hari wurin.